‘Ya ‘Yan Jam’iyyar PDP Sun Yi Tattakin Nuna Goyon Baya Ga Atiku Abubakar Da Sanata Yakubu Lado A Katsina
Dubun dubatar magoya bayan jami’yyar PDP da kimanin kungiyoyi 72 ne suka fito wani tattaki na nuna goyon baya da kuma samar da jama’a cewa ruhin jami’yyar PDP na cigaba da wanzuwa a dukkanin sako da lungu a ƙasar na.
Wannan tattaki na nuna goyon baya na zuwa ne kwanaki kadan da jami’yyar PDP zata fara yakin neman zaɓen ta a matakin gwamna da sauran kujeru a ranar 4/02023 a garin Funtua ta jihar Katsina.
Kazalika an fara wannan tattaki da kungiyar arewa Decide 2023 suka jagoranta domin nuna kauna da goyon baya ga ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyar PDP Atiku Abubakar da Sanata Yakubu Lado na Katsina.
An fara wannan tattaki da misalin karfe goma na safiyar juma’a daga kwanar liyafa inda suka biya zuwa shatale-talen liyafa zuwa shalkwatar jami’yyar PDP ta Katsina.
A lokacin gudanar da wannan kwarya kwaryar tattaki an yi layi sannan aka sahu da dubun dubatar magoya bayan jami’yyar PDP maza da mata suna rera wakokin da aka yi jami’yyar PDP da kuma ‘yan takara.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar reshen jihar Katsina, Comrade Kabir Umar Gambo, yace tattakin ya samu goyon bayan sama da ƙungiyoyi 74 na jam’iyyar PDP a Katsina.
Yace suna bi jiha-jiha ne a faɗin Arewacin Najeriya domin wayar da kan jama’a, tare da nuna nagartar Atiku Abubakar a matsayin shugaban ƙasa.
Sannan yayi kira ga gwamnoni 5 na PDP da suka fanɗare su dawo a haɗa kai domin a ciyar da ƙasar nan gaba, yace kowanne gida ana iya samun rabe-raben kai bare jam’iyyun siyasa.
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Katsina, Alhaji Lawal Ɗanɓaci, wanda ya samu wakilcin Ibrahim Galadima, ya nuna farin cikinsa game da ƙungiyar, duba da yadda take aiki tuƙuru don ganin Atiku Abubakar ya kai ga gaci.
Tsohon ɗantakarar Chairman na Katsina a jam’iyyar PDP Sanusi Audu Fari, yace lokaci yayi da za su yi waje da jam’iyyar APC a ƙasar nan baki ɗaya.
Yace idan kowa yayi tunani da ƙwalwar da Allah ya masa zai san cewa ci-baya ne aka samu ba cigaba ba a mulkin jam’iyyar APC.
