Wane Hali Aminu Darma Yake Ciki Bayan ‘Yan Fashi Sun Kai Masa Hari: Maiwada Ɗammallam Ya Yi Ƙarin Haske.
Na samu ganin Aminu Darma a Umaru Musa University Teaching Hospital, Katsina bayan Ɓarayi sun tarbe shi, sunyi mashi fashi dazu da misalin ƙarfe Goma Sha Biyu 12pm na rana.
Ɓarayin sun biyo shi daga banki ne, inda suka tarbe shi a daidai sha talai-talai na KSRC, da ya fahimci Ɓarayi ne, yayi ƙoƙarin tserewa, ya juyo ya sake komawa cikin gari. Ɓarayin basu hakura ba, sun biyo shi a guje har suka kawo inda ababen hawa suka hana shi ci gaba da tseren.
A ƙarshe, motar ta ƙwace mashi ta kuma bugi wani abu a bakin Titi Anan suka iske shi, suka harbe shi sannan suka ƙwashe Kuɗin. Yanzu haka na bar shi yana samun sauki; jami’an Asibitin suna yi mashi aiki a hannun da aka harbe shi.
Ina rokon Allah Ya bashi lafiya, Ya tsare gaba, Ya kuma kawo mana ƙarshen wadannan fitintinun Amin.
Malam Aminu Allah ya saka maka ya toni Asirin ko suwanene, Allah ya kyauta gaba Amin
