Waƙoƙin Batsa: Kotu Na Neman ‘Yan Kannywood 7 Ruwa A Jallo
Kotu ta umarci ƴan sanda su cafko su Ado Gwanja, Safara’u, Mr 442, Murja Kunya, Ummi Shakira da sauransu domin bincike
T@wagar wasu lauyoyi sun maka wasu gungun mutane da ake zargi da yada Alfasha a cikin al’umma a Kotu, wadanda suka hada da mawaki Ado Gwanja, Mr 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Murja Ibrahim Kunya, Ummi Shakira, Samha M. Inuwa da kuma Babiyana.
Cikin wata takarda da kotun majistare dake Bichi, karkashin mai shari’a, Jostis Bello Musa Khalid, an bukaci kwamishinan yan sanda na jihar Kano, ya gudanar da bincike akan wadanda ake zargi.
Tunda fari dai wani lauya ne mai suna Barista Badamasi Sulaiman Gandu Esq, ne ya bada wa’adin kwanaki uku ga hukumomin da abun ya sha fa akan su dauki mataki ga mawakin Hausa Ado Gwanja, akan wata sabuwar waka da yayi mai taken “Chas” wacce ake zargin anyi amfani da kalaman batsa a cikinta, idan kuma ba haka ba zai garzaya kotu.
To sai dai yanzu a iya cewa lamarin ya girmama, domin a cikin kunshin lauyoyin da suka maka wadancan Mutane a kotu, bayan barista Badamasi, akwai, Barista Muhd Ali Hamza Esq, Abba Mahmud Esq, Muhd Nasir Esq, L.T Dayi Esq, da kuma G.A Badawi.
Daga Cikin abubuwan da akayi kara akansu sun hada da yin wasu wakoki da sukayi karo da addini da kuma al’ada, masu ta ken “War” da kuma “Chas” wanda Ado Isa Gwanja yayi, sai kuma sauran da ake zarginsu da hawa kan wakoki suna tikar rawa da kuma wasu abubuwa da suka ci karo da addinin musulunci da kuma al’ada.
