September 18, 2026

Tunibu Ya Amince a Dauki Ma’aikatan Gandun Daji 1,000 Domin Magance Matsalolin Tsaro A Katsina -Dikko Raɗɗa 

FB_IMG_1775370540069

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki ma’aikatan gandun daji mutum 1,000 waɗanda za su tsare dazuzukan da ke fama da matsalolin tsaron a jihar baƙi ɗaya

 

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana haka a jin kaɗan bayan kammala wani taron gaggawa da yi da Malamai a Katsina

 

Gwamnan jihar Katsina ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu da kansa ya amince a ɗauki ma’aikatan gandun daji guda dubu ɗaya, domin tsare dazuzuka a jihar Katsina.

 

“Ina miƙa godiya ta bisa wannan al’amari na amincewar shugaban ƙasa da ya amsa rokon mu na ɗaukar ma’aikatan gandun daji 1,000 wanda za a ɗauki matasa maza da mata wanda kuma za su yi aiki tare da hukumomin tsaro” inji shi

 

Ya ƙara da cewa ɗaukar ma’aikatan zai samar da yanayi mai kyau na sauke nauyin da ya rataya akan su na tsare al’umma da gandun daji a fadin jihar Katsina

 

Gwamnan wanda ya nuna irin ƙoƙarin da ake yi na ganin an kawo ƙarshen matsalolin tsaro ta hanyar haɗa kai da Malaman Addini a matsayin wani ɓangare da za a iya samun cigaba da zaman lafiya tare da lalubo hanyar magance matsalolin tsaro.

 

Dikko Raɗɗa wanda ya ce tattaunawa da malamai ya zama wajibi domin ta haka ne za su san girman matsalar tsaro tare da neman hanyar warware matsalolin ta fuskoki da dama.

 

Ya ce dalilin wannan zama da malaman addini shi ne domin su ji kai tsaye daga wajen Malaman sannan su fahimci yanayin halin tsaro da ake ciki daga ƙarshe a nemi shawarar su wajan magance ta.

 

Ya ƙara da cewa girman wannan matsala ta kai inda ba za a iya barin jami’an tsaro da ita ba su kaɗai, shigowar al’umma musamman malamai zai zama hanyar samun zaman lafiya

 

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewa akwai masu taimakon ‘yan bindiga a cikin al’umma, ta hanyar bada bayanan sirri da kuma sayar da shanun da aka ɓarayin dajin suka sato

 

“Sannan da yawan waɗanda ke kai masu bayanai tare da sayar masu da shanun da suka sato, mutane ne da ake zaune da su wuri ɗaya, wannan tasa ake da buƙatar wayar da kan al’umma ta yadda kowa zai bada tasa gudunmawa.” Inji shi

 

Ya bayyana cewa malamai wani alami ne na bunƙasa zaman lafiya saboda kokarin su na bayar da tarbiyya da kuma daidaita al’amurra, saboda haka akwai bukatar su sanya hannu wajen maganin matsalar tsaro

 

Kazalika gwamna Raɗɗa ya yabawa gwamantin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu saboda taimakon da ta yi na ƙara turo jami’an tsaro a jihar Katsina

 

“Yanzu mun ƙara samun jami’an tsaro da dama da suka haɗa da sojoji da ‘yan sanda da jami’an hukumar farin kaya ta DSS wanda hakan ke ƙara karfafa mana gwiwa cewa dole mu nuna godiya kwarai da gaske” inji shi

 

Daga ƙarshe ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su kasance masu lura da abubuwan da ke zuwa suna dawowa domin ta haka ne za taimakawa gwamnati wajen dawowa da zaman lafiya.

About The Author