September 18, 2026

Tafiyar Atiku Abubakar Ta Neman Shugaban Ƙasar Najeriya Akwai Haske So Sai – Sarkin Katsina.

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya bayyana tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a matsayin tafiya da ake gaske haske so sai a cikin ta.

Mai Martaba Sarkin ya yi wannan kalami ne a lokacin da ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar PDP ya kai masa ziyarar ban girma a fadar da ke Katsina domin neman shawara da kuma addu’oi irin na manya.

Sarkin na Katsina ya ce wasu daga cikin kudirorin ɗan takarar sun buge shi matuƙa musamman batun inganta harkar tsaro da kuma tattalin arziki ta hanyar buɗe kan iyakokin Najeriya.

Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya ce yin haka zai taimaka gaya wajan farfaɗo da tattalin arziki da kuma shawo kan matsalar tsaro da ta adabin yankin arewa musamman jihar Katsina

“Babu ranar da ba za a bugu Mani waya a gaya mani cewa an sace mutane ko an kashe ba, babu ranar, wanda har hakan ta sa har neman lafiya sai da na je ƙasar waje saboda yadda wannan matsala ke damu na kullum” inji shi

Mai Martaba Sarki ya ce su iyaye ne ba ‘yan siyasa ba saboda haka duk wanda yake manufofi masu kyau ga Najeriya da kuma ita kanta Najeriya suna yi masa fatan alheri kuma za su riƙa bada shawara inda suka ga an kauce hanya

Ya kuma nuna jin dadin sa musamman yadda ɗan takarar ya je har ƙasar Birtaniya domin duba sarki lokacin da yake kwanshe a can, ya kuma nuna farin cikinsa akan wannan ziyara da aka kawo masa.

Tunda farko da ya ke faɗin dalilin wannan ziyara tasa a masarautar Katsina, ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce sun zo fadar Sarkin Katsina ne domin neman shawara da tabaraki ga iyayen ƙasa sarakuna.

Atiku Abubakar wanda ya ce daman ɗan gida ne saboda haka babu buƙatar yin dogon bayani akan irin ƙudirinsa idan ya samu nasara, amma dai yana kudirin inganta harkar tsaro da tattalin arziki musamman buɗe kan iyakokin Najeriya

Haka kuma Atiku Abubakar ya maida tallafin kuɗi har naira miliyan 50 ga waɗanda iftila’in hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a jihar Katsina.

Ya kuma sha alwashin inganta harkokin kiwon lafiya da walwala da baiwa ilimi fifiko mai girma gaske, idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *