September 18, 2026

Abuja Ta Samu Sabon Kwamishinan Yan Sanda.

0

Babban Sufeton yan sandan Najeriya Usman Baba, ya nada ma babban birnin tarayya Abuja sabon kwamishinan ‘yan sanda Sadiq Idris Abubakar. Wanda aka naɗan ya amshi aiki ne daga hannun Babaji Sunday da aka mayar da shi wani sashen rundunar.

Abubakar tun lokacin da ya hau kan karagar mulki ya baiwa mazauna jihar tabbacin inganta tsaro, tare da gargadin masu aikata laifuka da su nisanta kansu daga babban birnin kasar.

Kuma mamba ne a Cibiyar NIPSS dake Kuru-Jos, sannan yana da digirin digirgir a Jami’ar Abuja. Ya kuma yi digirin farko na Ilimin Kimiyya (BSc.Ed) a Jami’ar Usman Danfodiyo Sokoto.

Ya shiga aikin dan sandan Najeriya a shekarar 1992, a matsayin ASP, kuma tun daga nan ya yi aiki a fannoni daban-daban na rundunar yan sandan. Wuraren da ya yi aiki sun hada da; kwamandan rundunar yan Sandan kwantar da tarzoma ta 15 dake Ilorin, Jihar Kwara; babban jami’in dake bada horo, daraktan ayyukan wanzar da zaman lafiya a hedkwatar rundunar dake Abuja; kwamandan rundunar ‘yan sanda a Guinea Bissau, rundunar ECOWAS; da kuma Kwamandan kwalejin bada horo ta Ila-Orangun, Jihar Osun.

Ya kasance kwamishinan ayyukan wanzar da zaman lafiya na ’yan sanda kuma kodineta na rundunar ‘yan sanda ta musamman kafin a naɗa shi.

CP Sadiq ya halarci tarukan kara wa juna sani da tarurrukan bita a ciki da wajen Najeriya.

CP SADIQ, yayin da yake mika godiyarsa ga babban sufeton yan sandan Najeriya bisa wannan matsayi, ya kuma baiwa mazauna birnin tarayya Abuja tabbacin inganta tsaro. Hakazalika, ya kuma gargadi masu aikata laifuka a cikin babban birnin tarayya Abuja da su bari.

A halin da ake ciki, CP ya yi kira ga mazauna yankin da su ci gaba da taimaka ma jami’an ‘yan sanda, inji jaridar Vanguard dake zama majiyar Popular News Hausa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *