Shugaban karamar hukumar Charanchi ya kaddamar da sabon masallacin Juma’a a Kaɗanya.
Shugaban karamar hukumar Ibrahim Sani ya ce addinin Muslunci koyar da zaman lafiya da san juna ya ke.
A sakonshi, shugaban kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam Sheik Ishaq Nuhu Batagarawa ya hori mutanen yankin da cewa su kula da masallacin yadda ya kamata.
Shugaban kungiyar wanda Ustaz Abbas Musa Abubakar ya wakilta, ya bukaci mutane da su nemi ilimin addinin Musulunci.
A jawabin wanda ya gina masallacin Umar Isyaku Kaɗanya, ya yaba ma wadanda suka taimaka aka kammala shi.
Limamin sabon masallacin Malam Auwal Yunusa da Shugaban Munazzamatu na yankin Malam Amadu Lawal sun yaba ma wanda ya gina masallacin.
Sarkin Shanun Katsina hakimin Charanchi Abashe Abdulkadir wanda ya yi jawabi ta bakin Babangida Abashe, ya mika sakon shi na godiya.
Kuma daga nan mataimakin limamin babban masallaci Katsina Dayyabu Liman ya jagoranci sallar Juma’a raka biyu.
