Hakimin Mani Ya Yi Kira Ga Masu Hannu Da Shuni Su Maida Hankali Ga Sadakatul Jariya.
Durbin Katsina hakimin Mani ya yi kira ga masu hannu da shuni da su maida hankali kan ayyukan sadakatul jariya.
Umar Babani Isah ya yi wannan kiran a lokacin kaddamar da sabon masallacin Juma’a a garin Kartakar dake cikin karamar hukumar Mani.
Ya yaba ma masu taimakon al’ummar da suka hada da Hajiya Jamila Duwan, da al’ummomin yankin, dama kungiyar Fitiyanul Islam bisa gina masallacin.
Ya kuma bukaci mutanen garin da makwabtansu da su rika yin sallolinsu cikin masallacin kowane lokaci.
Haka nan kuma, shugaban karamar hukumar Dr. Yunusa Bagiwa ya yaba ma kokarin masu ruwa da tsaki wurin yaɗa addinin Islama a yankin.
Tare da bayyana cewa, gwamnatin jiha ta gina hadi da gyara masallatai da kuma makarantun Islamiyyu don bunkasa addinin Islama a yankin.
Ya bayyana bukatar ganin masu hali na taimaka ma mabukata dake cikin al’umma.
Tunda farko, saida mataimakin limamin masallacin Juma’a na Katsina malam Habibu ya jagoranci sallar Juma’a ta farko a masallacin.
Kuma a jawabansu na daban daban malam Lawal Kuraye, da Malam Ibrahim Bindawa da kuma malama Murja Duwan sun yi kira da a samu hadin kai tsakanin al’ummar musulmi a yankin.
Daga karshe dai hakimin yankin ya nada malam Lawal Kartakar a matsayin babban limamin sabon masallacin Juma’ar.
