Shekara 8 kana mulki amma ƴan Kwankwasiyya su ka kwace gwamnati a hannunka: Adeleke ya yi wa Ganduje shaguɓe
Shekara 8 kana mulki amma ƴan Kwankwasiyya su ka kwace gwamnati a hannunka: Adeleke ya yi wa Ganduje shaguɓe
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya caccaki Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, kan maganganunsa game da shirin jam’iyyar na kwace ikon jihohin Osun da Oyo bayan nasararta a zaben gwamna na Jihar Ondo.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa, bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a Ondo, Ganduje ya bayyana cewa APC ta fara shirye-shiryen kwace ikon jihohin Oyo da Osun, wadanda a halin yanzu ke karkashin ikon jam’iyyar PDP.
A martaninsa, Adeleke ya ce kalaman na Ganduje wata manufa ce ta tada zaune tsaye a yankin Kudu maso Yamma tare da haddasa rikici.
Ta bakin mai magana da yawunsa, Olawale Rasheed, Adeleke ya bayyana a a yau Litinin cewa maganganun da shugaban APC ya yi sun saɓawa dimokuradiyya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ikirarin tsayawa kai.
Adeleke ya yi wa Ganduje shagube, yana mai cewa ya kasa kare Jihar Kano daga hannun kungiyar Kwankwasiyya, wadda ta kayar da jam’iyyar da duk da yana mulkin jihar tsawon shekaru takwas.
“Idan har Ganduje na son Shugaban Kasa da gaske, me ya sa yake kokarin tada hankali a yankin Kudu maso Yamma, inda Shugaban Kasa ya fito, ta hanyar yin barazanar karya dokar zabe da kuma tauye hakkin masu zabe?”
