Obasanjo ba shi da kimar sukar shugaba Tinubu – Fadar gwamnatin Nijeriya
Obasanjo ba shi da ƙimar sukar shugaba Tinubu – Fadar gwamnatin Nijeriya
Fadar shugaban Najeriya ta ce tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba a bin koyi bane, saboda yadda yake neman daukaka darajarsa a idon jama’a da kuma cacakar duk wani shugaba da ya biyo bayansa.
Sanarwar da mai magana da yawun shugaban Sunday Dare ya gabatar ya bayyana Obasanjo a matsayin wanda ba shi da aikin yi sai sukar mutanen da suka samu madafin iko saboda matsalolin da suak adadbi kasar.
Dare yace bayan gazawar da gwamnatinsa ta yi, Obasanjo ya shirya zabe mafi muni a tarihin Najeriya wajen bai wa marigayi Umaru Musa Yar Adua dama zama shugaban kasa, wanda shi da kansa ya amsa cewar zaben da ya kawo shi karaga ba shi da inganci.
Dare ya zargi Obasanjo da kasa samarwa Najeriya shirin tsaron kasa mai inganci, abinda ya kai ga sojojin Najeriya sun gaza samun kayan aiki har zuwa lokacin da Muhammadu Buhari ya hau karagar mulki, ya kuma saya sojoji sama da jiragen sama 40 na yaki, cikin su harda Super Tucano 12 da jirgin yaki na ruwa domin yaki da ‘yan ta’adda.
Mai magana da yawun shugaban yace ‘yan Najeriya ba zasu manta da badakalar kudaden da aka gani tsakanin Obasanjo da mataimakinsa Atiku abubakar a hukumar PTDF ba, tare da kuma barnatar da dala biliyan 16 wajen samar da wutar lantarki amma suka bar yan Najeriya cikin duhu.
Dare yace inda Obasanjo ya yi aikinsa yadda ya dace, da Najeriya bata samu kanta a halin da take ciki yanzu ba. Idan dai ba’a manta ba, a makon jiya Obasanjo ya bayyana cewar duk wasu cika cikan rugujewar kasar sun tabbata a karkashin gwamnatin Bola Tinubu.
📷Premium Times
