Shariar Mahdi Da Kamfanin NAK: Kuto Ta Sanya Ranar 7 Ga Watan 3 A Kammala Sauraran Karar.
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina.
Baban kotun majistire ta daya da ke zama a Katsina ta daga shari’ar da ake tabkawa tsakanin kamfanin NAK da ke Funtua da kuma Barista Mahdi Sa’idu akan zargin sojan gona da yin gaban kai da kuma cutarwa.
Tunda da farko dan sanda mai gabatar da kara ASP ANTAK Bawa ya shaidawa kotu cewa wannan shari’a ce da ake yi tsakanin kamfanin NAK da kuma Barista Mahdi akan zargin sojan gona da cutarwa inda aka sa yau alhamis domin kammala sauraran karar.
Haka kuma ya cigaba da shaidawa kotu cewa wannan laifi ne da ake zargin Mahdi Sa’idu da ya sabawa sashe na 324 da 323 da 364 da kuma 368 na kudin laifuffuka da hukuncin su na final koda.
Sai dai kuma Barista Mahdi Sa’idu ya shaidawa kotu cewa lauyan da ke kareshi yana halartar wata shari’a a bar kotun jiha ta 3 saboda haka yana san a daga zuwa wani lokaci domin cigaba da sauraran karar.
Mahdi Sa’idu ya ce domin a samu adalcin shari’a yana rokon kotu da ta dage wannan sauraran karar zuwa lokaci saboda lauyasa yana gaban babar kotun jiha ta 3.
‘Banga yadda za a cigaba da sauraran karar ba alhali lauyan da ke tsaya mani baya kusa da ni saboda haka sai dai idan kotu zata dage wannan zama zuwa lokaci da ya yi mata domin a cigaba da sauraran karar’ inji Mahdi.
Shi kuwa a nashi martanin dan sanda mai gabatar da kara ASP ANTAK Bawa ya ce bai amince da wannan roko ba na Barista Mahdi Sa’idu saboda yadda aka rika dage wannan shari’a kusan sau uku ke nan saboda haka yana rokon kotu ta yi abinda ya da ce.
Ya kara da cewa rokon da zai kara yi shi ne tunda lauyan wanda ake kara zai bar baban kotun jiha ta uku da misalin karfe 12:30 na rana a daga shari’ar zuwa wannan lokaci.
Sai dai kuma a nata hukuncin alkaliyar baban kotun majistire ta daya Hadiza Danja ta bada hukuncin cewa saboda a samu adalcin shari’a ta maida wannan zama zuwa ranar 7 ga watan 3 domin karkare sauraran wannan kara.
Idan za a iya tunawa anyi karar Barista Mahdi Sa’idu ne bisa zargin yin sojan gona da kamfanin NAK da ke Funtua ya kai inda ya yi amfani da hatimin kamfanin ya janye wata shari’a da kamfanin ke yi da wani a matsayin na lauyan kamfanin ba tare da masaniyar hukumar gudanarwa ta kamfanin ba.
Haka kuma Barista Mahdi Sa’idu an yi zargin ya gabatar da kansa a matsayin sakataran kamfanin NAK wanda jami’an kamfanin ke ganin suna da shari’ar da za su yi da shi domin neman hakki.
