Satar Mai: Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur Ya Ziyarci Jihar Imo.
Gwamnatin Najeriya ta ce tana daukar matakan dakile satar danyen mai da fasa bututun mai a kasar.
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva wanda ya kai ziyara jihar Imo mai arzikin man fetur da iskar gas a yankin Kudu maso Gabas, yana son gwamna Hope Uzodimma ya hada kai da sauran hukumomi domin dakile ayyukan ta’addancin, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta AIT.
A ziyarar da Ministan ya kai akwai babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Manjo Janar Lucky Irabor, da kuma Babban Manajin Darakta na Kamfanin NNPC, Mele Kyari, da sauransu.
A cewar Sylva, sun kai ziyarar ne domin tabbatar da cewa gwamnatin jihar Imo da al’ummomin dake hako mai sun hada hannu wajen kawo karshen ayyukan satar man fetur ba bisa ka’ida ba, wanda yake illa ga tattalin arzikin kasar.
Babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, Maj.-Gen. Lucky Irabor, ya bayyana cewa ziyarar ta zama wajibi biyo bayan dimbin asarar tattalin arziki da ake fuskanta a bangaren mai da iskar gas.
Gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma ya kuma yi kira da a hada kai da masu ruwa da tsaki wajen kawar da barna a fannin.
Uzodimma ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kara tsaurara matakan tsaro a kan layukan bututun mai, tare da yin alkawarin tallafa wa kamfanonin dake hako mai a Jihar a kokarin dakile ayyukan da ba su dace ba a bangaren mai da iskar gas.
