September 18, 2026

Sanata Ibrahim Ida Ya Maye Gurbin Wazirin Katsina Sani Abubakar Lugga

0

Sanata Ida shi ne yake rike da sarautar Sardaunan Katsina kafin nadin nasa.

Sanata Ida shi ne yake rike da sarautar Sardaunan Katsina kafin nadin nasa.

An ba tsohon dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mohammed Ida a matsayin Wazirin Katsina.

Sarkin Yaƙin Katsina kuma sakataren masarautar Alhaji Bello Mamman Ifo ne ya tabbatar wa BBC ranar Talata.

Sanata Ida ya maye gurbin Alhaji Sani Abubakar Lugga wanda ya yi murabus daga muƙaminsa na Wazirin Katsina a watan jiya.

Sanata Ida shi ne yake rike da sarautar Sardaunan Katsina kafin nadin nasa.

An haifi Sanata Ida a birnin Katsina a shekarar 1949, kuma ya yi karatunsa na boko a Najeriya da Birataniya da kuma Amurka.

Sabon Wazirin na Katsina ya soma aikin gwamnati da Babban Bankin Najeriya, kuma ya rike mukamai da dama a gwamnati, ciki har da Babban Sakatare na Ma’aikatar Tsaron Najeriya.

Sannan ya wakilci shiyyar Katsina ta Tsakiya a majalisar dattawan kasar tsakanin 2007-2011.

Sanata Ida yana da mata daya Hajiya Khadija da ‘ya’ya da jikoki da dama.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *