Sanata Baba Kaita Ga Gwamna Masari: In Kaki Sharar Masallaci Ka Yi Ta Kasuwa
Shekara ‘dai ‘dai har shidda bayan senatoci da ‘yan majalisar tarraya dana majalisar jiha mun rungumi Al’qurani mai tsarki da alqawalin tabbatar da adalci Kan sarrafa kudaden al’umma, tafiyar batai nisa ba kwatsam muna dafa madafan iko kuma alert ya fara shiga account sai muka shafa hoda mukai mursisi muka koma fadanci banbadanci da tumasanci da nuna halin “ko in kula”, muka bar gwamna Aminu Bello masari yaqi yin zaben local governments under the pretext na litigations.
Daga nan kau akai ta sharholiya da daruruwan biliyoyin qananan hukomomi duk kau da masaniyar halin da aqubar da jama’ar da suka zabo mu a qananan hukomomin suke ciki.
Kwadayin mulki da cin amana yasa muka kama bakunan mu mukai muqqui, kodayake a bayan fage dukkan mu ban cirewa kowa hula ba muna nuna takaici da nuna rashin jin dadi abinda ke faruwa a jiharmu Kai wasu ma hadda zage zage.
KWATSAM jiya sai ga goron gayya daga gwamna zai zauna da senatoci da ‘yan majalisa tarayya wanda kira bayan kira nace ban zuwa.
GA MUHIMMAN LABARAN WANDA NAN TAKE SUNA GAMAWA HAR NA FARA BARCI AKA TASHENI AKA GUTSURA MAN.
1) electoral act …. (topic for another day)
2) local government elections wanda Gwamna yaqi yi a lokacin da al’ummar da suka zabo mu dashi kanshi suke cikin baqar aquba da kuma buqatar zaben don rage radadi da kuma inganta rayuwarsu babu kamar harkar tsaro data addabi jihar.
Abun al’ajabi takaici da baqin ciki shine yadda Gwamna yasa kafa ya shure maganar zaben inda ya bar mutane cikin aquba da matsaloli kala kala. kuma aka kasa ganin inda kudaden suka zurare suka shige a duk fadin jihar, bayan kwashe shekara shidda curr, ba’a maganar basussuka da aka ciwo.
Yau sai gashi yana karkarwa da zumudi kai harma da kokarin yiwa dokar zabe karan tsaye a inda yake ganin shi zai iya dibar wa kansa wa’adi daya gadama don kawai yanzu ya shirya zabe.
Ko ina aka samo kudin da za’a shirya zaben yanzun? wadanda da can baya babu su.
Ko minene ya chanza bayan kiranye kiranye da talakkawan katsina suka share shekara sama da shidda su nayi in ari kalmar bakin gwamna da yana neman zabe “don a sakar masu mara”?Amma yay kunnen Uwar shaggu dasu.
Dalilin zumudin shine duk local government din da bata da zababbu toh zatai wa kanta gibi’ wajen kawo delegates na APC national convention wanda ranarsa take tallagurgur amma ake tsamanin yinsa a February.
Gwamna yasan kwanan zancen yasan kwadayin kujera wajen bama yan majalisa kadai ba mafi yawancin masu muqami ana iya juwa su suyi abinda akeso suyi don a samu biyan buqata. Saboda haka yanzun gwamna ya tashi yin zabe bisa ga son zuciya kowa sai ya hau layi.
TIRR da halin mu nacin amanar jama’ar da suka zabe mu dashi kanshi Gwamnan, muna Ina aka share shekara shidda aka gaza yin zabe a katsina? Wanda duk fadin jihohin nigeriya ba jihar da batai zabe ba kuma jihar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito kuma duk da sanin matsayar shi akan zaben qananan hukumomi, sai don yanzun ana son ai kwanta kwanta da delegate wadanda za ai cinikinsu nan gaba kadan shine za’a kirkiri zabe yanzu yanzu ….
Muna iya cin amanar dunbin jama’a muqi abinda suke so kuma ko da buqatar tasu maslahar al’umma ce a hannu daya a dayan hanun kuma muna iya komi harda almubazaranci da dukiyar jama’a don biyan buqatar kanmu, Allah ya sawwaqa, dadin abun akwai gobe qiyama.
Ina tunawa da cin kashin da muka yiwa PDP amma don rashin kunya da tumasanci jama’a sun yarje mana sun bamu amana suna ganin zamu iya sallah amma kash abun takaici gashi mun kasa alwalla.
Daga shafin Sanata Ahmad Baba Kaita
