Rundunar ‘Yan Sandan Katsina Ta Cika Hannu Da Masu Satar Wayoyin Lantarki
Rundunar ‘Yan Sandan Katsina Ta Cika Hannu Da Masu Satar Wayoyin Lantarki
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar cafke mutane biyu bisa zargin cire wayoyin gwamanti tare da lalata su.
Kakakin rundunar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana haka a lokacin da yake hulan masu laifi daban-daban a shalkwatar ‘yan sanda da ke Katsina.
Ya bayyana cewa an kama Umar Muhammad ɗan shekara 25 mazaunin sabuwar unguwa Katsina akan zargin Lalata Wayoyin Wuta da kuma sace su.
“Baturen ‘yan sanda na garin Ɓatagarawa ya samu labarin ana tone wayar akan hanyar kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman inda ya tura jami’an tsaro kuma suka yi nasarar cika hannu da ɓarayi.
Ya ƙara da cewa a lokacin bincike an samu diga da shebir da abin yanke waya da zarto guda biyu, wanda kuma waɗanda ake zargi suka tabbatar da cewa sun yi haɗin baki da wssu mutane.
A cewar sa, mutanen sune; Isma’il da Aminu da Sama’ila Abdulrashid dukkan su yan Katsina ne kuma yanzu ana neman su ruwa a Hallo, kuma sun bayyana wani Mas’adu Amadu da ke sayen wayoyin da suke satowa.
Yanzu haka dai ana cigaba da bincike akan wannan lamari inji kakakin rundunar ASP Abubakar Sadiq Aliyu.
A wani labarin kuma rundunar ta ce ta samu nasarar kama Ahmad Suleiman a unguwar Abbatuwa cikin birnin Katsina wanda ake zargi da sace wayoyin gwamanti da kuma lalata su.
Ya ce a ranar 9 ga watan Augusta jami’an tsaro sun samu labarin an lalata tare sace wayoyin kamfanin mulmula karafa na NAK Steel Rolling Company, Katsina
Bayan samun wancan rahoton sirrin sun ƙaddamar da bincike wanda ya kai su ga samun nasarar damke wanda ake zargi Ahmad Suleiman ya sace wayoyin da suka kai na naira dubu ɗari biyar
Sai dai lokacin da jami’an Yan sanda ke gudanar da bincike akan lamarin wanda ake zargi ya tabbatar da aikata laifin sace wayoyin kamfanin NAK Katsina
