Hasashe: Ƙananan Hukumomi 6 Za su Fuskanci Ambaliya Ruwa A Katsina
Hasashe: Ƙananan Hukumomi 6 Za su Fuskanci Ambaliya Ruwa A Katsina
Gwamantin jihar Katsina ta bayyana cewa akwai yiwuwar wasu ƙananan hukumomi guda shida za su iya fuskantar ambaliyar ruwa kafin wucewar damina.
Sakataren gwamnatin jihar Katsina Barista Abdullahi Garba Faskari ya bayyana haka a Katsina a lokacin taron manema labarai da ya kira.
Barista Abdullahi Garba ya ƙara da ya zama wajibi a faɗakar da al’umma sakamakon rahotan da suka samu daga hukumar kula da yanayi ta NIMET ta yi hasashe a Katsina.
A cewar sa, ƙananan hukumomin da ake sa ran za su fuskanci ambaliyar ruwa sun haɗa da Katsina da Bakori da Bindawa da Funtua da Jibia da Daura da kuma Kaita
“Muna fatan masu ruwa da tsaki da suka haɗa da kwamishinan kiwon lafiya da ƙananan hukumomi da masarautu da kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa da kuma kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida domin samun nasarar fadakar da al’umma” inji shi
Ya ƙara da cewa sauran masu ruwa da tsaki sun haɗa da ma’aikatar Gona da kiwo da shugaban Hukumar bada agajin gaggawa ta jiha da hukumar tsaftace muhalli ta jiha da kuma ƙananan hukumomin ake sa ran za su fuskanci wannan matsala.
Barista Abdullahi Garba ya bayanin cewa za a yi aiki tare domin daukar mataki dan ganin wannan lamari bai afku ba ta hanyar fadakar da al’ummomi.
