September 18, 2026

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Yaba Da Ayyukan Kwamitin Jin Kai Da Ceto Na Ƙasa Da Ƙasa A Katsina 

IMG-20250625-WA0004

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Yaba Da Ayyukan Kwamitin Jin Kai Da Ceto Na Ƙasa Da Ƙasa A Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta yaba da irin ayyukan kwamitin jin kai na ƙasa da ƙasa wato “international Rescue Committee” wanda yake tallafawa al’ummar jihar Katsina
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bello Shehu ya yi wannan yabo a lokacin da kwamitin ya kai masa ziyarar ban girma a shalkwatal ‘yan sanda da ke Katsina.
CP Bello Shehu ya bayyana mahimmancin wannan kwamiti musamman shirye-shiryen da yake gudunmawa ga wasu al’ummomi waɗanda harin ‘yan bindiga ya shafa, inda ya bada tabbacin goyon bayan rundunar ‘yan sandan
Haka kuma ya kira ga kwamitin da ya bar kofofin shawarar sa a buɗe ta yadda za a samu haɗin gwiwa da sauran kungiyoyi domin cimma nasara.
Dangane da batun take hakkin ɗan adam CP Bello ya bada tabbaci ga wannan kwamiti da cewa yanzu haka sun samar da wani ɓangare sashen bincike da rundunar domin kula da wannan batun da sauran laifuffuka.
Tunda farko da yake jawabi shugaban kwamitin jin kai da ceto mista Elam ya bayyanawa CP Bello Shehu irin ƙoƙarin da wannan kwamiti ya yi da suka haɗa batun kiwon lafiya da bada tallafi da kuma samar da aminci a tsakanin al’umma
Mista Elam ya ƙara da cewa babban burin wannan kwamiti shi ne a samar da wani yanayi mai kyau ga al’ummomin da bala’in ‘yan bindiga ya ratsa da su musamman a arewa maso yamma
A cewar sa, yanzu sun fara aiki ne a wasu ƙananan hukumomi da suka haɗa da Ɓatagarawa da Batsari da kuma Katsina sannan ya yi ƙarin haske akan ƙoƙarin da kwamitin ke yi na ƙare hakkin ɗan adam
Daga ƙarshe mista Elam ya yi rokon ganin samun goyon bayan rundunar ‘yan sandan jihar Katsina domin samun nasarar tafiyar da wannan aiki na su

About The Author