Gidauniyar Mangal Ta Yi Wa Mutum 3,000 Masu Fama Da Lalurar Yo Yan Fitsari Aiki Kyauta a Katsina
Gidauniyar Mangal Ta Yi Wa Mutum 3,000 Masu Fama Da Lalurar Yo Yan Fitsari Aiki Kyauta a Katsina
Gidauniyar Mangal da ke Katsina ta kashe kuɗi fiye da naira miliyan 80 wajen ɗaukar nauyin mutum 3,000 masu lalurar yoyan fitsari domin yi masu aiki kyauta a jihar Katsina
Ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na gidauniyar Malam Hussaini Kabir ya tabbatar da haka ga manema labarai a Katsina
Malam Hussaini Kabir ya ƙara da cewa a wannan ɓangaren na masu lalurar yoyan fitsari an gudanar da irin wannan aiki sau goma ke nan daga lokaci zuwa lokaci inda kuma fiye da mutane 3,000 suka amfana da wannan tallafi.
A cewar sa, a lokacin da gudanar da wannan aiki a zango na biyu na wannan shekara an kashe fiye da naira miliyan 20 domin yi wa masu lalurar yoyan fitsari aiki da suka kai mutum 100
Kazalika Malam Hussaini Kabir ya yi bayanin cewa akwai marasa lafiyar da ba su buƙatar aiki waɗanda ake duba su ana ba su magunguna kuma kyauta ne daga gidauniyar Mangal
‘ Kamar yadda aka sani shi ne aikin tallafi ɗaya daga cikin nauyin da ya rataya a wuyan su tare da fatan hakan zai taimakawa al’umma musamman masu ƙaramin karfi ” inji shi
Sai dai Malam Hussaini ya ce, marasa lafiya daga ƙauyuka daban-daban da suka haɗa da wajen jihar Katsina da kuma jamhuriyar Nijar duk suna amfani da tallafi da karanci na gidauniyar Mangal.
Kamar yadda ya jaddada manufar yin waɗannan ayyuka shi ne a samarwa al’umma sauki kashe kuɗaɗe a ɓangaren kiwon lafiya domin su samu kulawa a matakin farko.
Haka kuma ana cigaba da wannan aiki yanzu haka a asibitin Ƙashi ta Amadi Rimi da ke cikin karamar hukumar Ɓatagarawa a jihar Katsina.
Ɗan kwamitin amintattu na gidauniyar Mangal ya ƙara da cewa an kirkiri wannan gidauniya a shekarar 2016 inda suka fara da yi wa al’umma kyauta da suka haɗa da aikin ido da aikin Ƙaba da gwaiwa inda zuwa yanzu dubban al’umma ne suka amfana
Malam Adamu Aliyu yana ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da wannan tallafi wanda kuma ma’aikaci ne a kwalejin kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina ya yaba da ƙoƙarin wannan gidauniya, inda ya ce tuni yake neman irin wannan taimako sai yanzu ya samu.
Yana mai cewa albashin da yake ɗauka ba zai isa ya dauki nauyin kansa har ayi masa wannan aiki ba, sai ya yi addu’ar Allah ya sakawa waɗanda suka assasa wannan aikin alheri.
