NIS Zata Yi Hadin Gwiwa Da ‘Anti-Drugs Campaign Network’ Wajen Magance shaye-shaye A Katsina
Hukumar shige da fice ta Ƙasa ”NIS’ ta ce zata yi haɗin gwiwa da kungiyar masu fafutuka wajan ganin an kawo karshen matsalar shaye-shaye ta Anti-Drugs campaign network domin samun nasara.
Shugaban hukumar NIS a jihar Katsina, Alhaji Ahmad Tijjani Mohammed ne ya bayyana haka a lokacin da kungiyar ta kai masa ziyarar ban girma tare da neman haɗin kai domin yin wannan aiki mai ƙalubale da yawa
Haka kuma shugaban ya yi na’am da wannan yunkuri na ita kungiyar ‘Anti-Drugs Campaign Network’ da ta yi tunanin kirkiro da hanyoyin magance matsalolin shaye-shaye da suka zama ruwan dare gama duniya a wannan ƙasa.
“A namu ɓangaren kamar yadda muka saba, muna aiki tare da sauran hukumomin tsaro musamman akan iyakokin Nijeriya, to zamu cigaba da yi domin ganin an samu sauki wannan matsala da ta addabi al’umma.” Inji shi
Ahmad Tijjani Mohammed ya ce duk da kasancewar hukumar su tana iyakar nata hurumin akan abinda ya shafi ƙasa da ɗan ƙasa amma ya yi alƙawarin bada gudunmawa ga wannan kungiyar don a samu nasara.
Tunda da farko da take jawabin maƙasudin kai irin wannan ziyara, shugabar kungiyar ‘Anti-Drugs Campaign Network’ Hajiya Khadija Saulawa ta bayyana cewa mahimmancin hukumar NIS yasa suka zaɓi kawo ziyara domin neman shawara da gudunmawa idan buƙatar hakan ta taso
.Ta ƙara da cewa abinda ya jawo hankalin su domin samar da wannan yunkuri ƙarƙashin wannan kungiyar shine wata ƙididdiga da aka fitar wanda ta nuna cewa jihar Katsina ita ce ta biyu wajen ta’amoli da miyagun kwayoyi a Nijeriya.
“Wannan ƙididdiga ta yi matuƙar tada mana hankali a matsayin mu na ‘ yan jihar Katsina wanda hakan tasa muka yanke shawarar cewa ya kamata mu yi wani abu akan wannan matsala, tunda abu ne da ya shafi kowa da kowa” inji ta.
Hajiya Khadija Saulawa ta cigaba da cewa samar da inganciyyar al’umma da kuma maganin matsalar tsaro ya ta’alaƙa ne da samar da nagartatar al’umma wanda yanzu aka rasa.
Tana mai cewa, idan aka samu hukumomi irin su NIS da NDLEA da ‘Yan Sanda da Kwastom da sauran su, sun shiga cikin wannan tafiya hakika za a rage wannan matsala a cikin al’umma, hatta matsalar tsaro tana da alaƙa mai girma da harkar shaye-shaye.
Shugabar kungiyar ‘Anti-Drugs Campaign Network’ ta bayyana cewa sun kai irin wannan ziyara a hukumar NDLEA wanda ita ce ke da hankalin wannan aiki, sannan suna shirye-shiryen kai irin wannan ziyara ga sauran hukumomin tsaro da masarautun Katsina da Daura domin samun shawara
.Daga ƙarshe an gabatar da wani littafi da kungiyar ‘Anti-Drugs Campaign Network’ ta samar wannan zai taimaka wajen magance wannan matsala ga shugaban hukumar NIS na Katsina Ahmad Tijjani Mohammed.
