Gwamna Dikko Umar Ya Taya Kwamarad Dan Ali Murnar Zama Shugaban NUJ Mafi Kwazo a Arewa Maso Yamma.
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya taya shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa reshen jihar Katsina NUJ Tukur Dan Ali murnar zama shugaba mafi kwazo a shiyyar arewa maso yamma.
An dai bayyana Kwamarad Tukur Dan Ali a matsayin shugaban da yafi kowane kwazo a yankin arewa maso yamma wajen hidimar aikin jarida da kuma ‘yan jaridu.
Shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa mista Chris Isiguzo ne ya bayyana cewa Kwamarad Tukur Dan Ali ne shugaba mafi kwazo a wannan yanki a lokacin taron zartawar na kungiyar da aka gudanar a Abuja jiya Laraba.
Kamar yadda gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa a ɓangaren yaɗa labarai Ibrahim Kaula ya fitar tana cewa Kwamarad Tukur Dan Ali ya cancanci samun wannan ƙarramawa duba da irin salon shugabancin da yake yi wa kungiyar a jihar Katsina
Ya ƙara da cewa wannan ƙarramawa an ɗora ƙwarya a gurbin ta saboda haka yana taya shi murnar da iyalansa da kuma ‘yan jaridu na jihar Katsina baƙi ɗaya
