September 16, 2026

Najeriya Za Ta Yi Haɗin Gwiwa Da Jamhuriyar Cuba Wurin Samar Da Rigakafin Cututtuka.

0

Ministan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta Najeriya ya ce gwamnatin tarayya za ta yi haɗin gwiwa da jamhuriyar Cuba wurin samar da ruwan alluran rigakafin cututtuka.

Dr. Adeleke Mamora ne ya sanar da hakan a lokacin da jakadar kasar ta Cuba Mrs. Clara Pulido ta kai mashi ziyara a Abuja.

Ya ce, haɗin gwiwar zai bada dama a kafa irin kamfanonin dake samar da ruwan alluran rigakafin cututtukan kasar a Najeriya.


Ministan ya yi nuni da cewa, jamhuriyyar Cubar ta ci gaba sosai a bangaren kula da lafiya, ta yadda za ta iya taimaka ma Najeriya a bangaren kiwon lafiya don ganin ta ci gaba.

Dr. Adeleke Mamora ya ce samar da ruwan alluran rigakafin zai taimaka gaya wurin yaki da cututtuka a Najeriya da suka hada Masassara Cizon Sauro, Masassarar Lassa da kuma kyadar Biri.

Tunda farko, saida jakadar kasar Cubar Mrs. Clara Pulido ta yi fatan ganin an cimma kudurin samar da ruwan alluran rigakafin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *