Mutuwar Mutane 6 a Zamfara ya sanya Matawalle ya dakatar da taron yakin neman zaɓen sa.
Daga Hussaini Ibrahim
Gwamnan jiha Zamfara Hon,Bello Muhammed Matawalle ya dakatar da gangamin yakin neman zabensa a karamar hukumar Bukkuyum domin alhinin rasuwar wasu mutane takwas da suka yi mummunan hatsari a hanyar Gummi zuwa Bukkuyum a daren Juma’a.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka gwamnan kan wayar da kan Al’umma da yada labarai Zailani Bappa.
Sanarwar ta ce: “Hatsarin ya faru ne bayan Sallar Magariba inda wasu motoci uku suka yi artabu da juna inda suka kashe mutane shida da suka hada da sabbin ma’aurata”.
Sanarwar ta ce, biyar daga cikin gawarwakin an yi musu zana’ida bayan salar Juma’a a garin Bukkuyum da yammacin yau inda mai martaba da tawagarsa suka halarta.
Mahangar Arewa ,ta ruwaito cewa, tun da farko an bukaci Gwamna Matawalle da ya kaddamar da gangamin yakin neman zabensa a Bukkuyum bayan Sallar Juma’a, amma ya yanke shawarar dakatar da taron domin girmama rayukan al’ummar jihar da suka rasu.
A maimakon haka sai ya ziyarci mai martaba sarkin Alhaji Muhammad Usman a fadarsa tare da mika ta’aziyya ga iyalai da al’ummar garin Bukkuyum baki daya.
Ya ce Allah madaukakin sarki ne ya tsara haka cikin hikimarsa, kuma hukunci Allah shine mafi alherin zabi ga muminai.
Kafin ya tashi daga fadar, Gwamna Matawalle ya nada tsohon mataimakin gwamnan jihar, Malam Ibrahim Wakkala Liman da ya gabatar da addu’a ta musamman.
