September 19, 2026

Mutane 970 Ke Karatun Digiri A Cibiyoyin Gyaran Hali Da Dama A Najeriya

0

Daga Awwal isah, Katsina

Mazauna gidan gyaran hali wanda aka fi sani da gidan yari 970 ne ke karatun degree a cibiyoyin gyaran hali daban daban dake faɗin ƙasar nan.

Baban konturolan hukumar gidajen gyaran halin da ke ƙasar nan Halliru Nababa ya bayyana haka a Abuja.

Kuma ya bayyana cewa, mazauna gidajen gyaran halin da dame ne suka rubuta jarabawar kammala makarantar secondary da ta haɗa da WAEC da NECO, tare da samun sakamako mai kau.

Halliru Nababa ya ce lokaci ya wuce na kallon gidajen gyaran hali a matsayin wuraren hukunci ko kuma wurin maida mutane marasa amfani a rayuwa.

Kamar yadda ya bayyana, hukumar ta maida hankali kan horas da mazauna gidajen gyaran halin don ganin idan sun dawo cikin yan uwansu, sun zama mutanen kirki.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *