November 17, 2026

Mutane 313 Suka Amfana Da Tallafin Gidauniyar Alqamat Brains Box Solution Da Miliyan 300

0

Babangida Sunusi, Kano

Kimanin matasa dari da sha ukku ne suka samu tallafin kudi naira milyan biyu-biyu da gidaunyar Alkamat Brains Box ajahar Kano dan inganta harkokin kasuwancinsu

Hakan na zuwa ne a bakin shugaban gidauniyar Alkamat Brains Box watau matashi kuma dan kishin al’umma Alkamatu Hussaini.

Yana wannan bayyani ne ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron kara wayarma da al’umma kai kan mahimmanci rike sana’a komin karantarta

Alkamatu Hussaini ya kuma bayyana cewa kada mutum ya samu kasawa a duk lokacin da yasa wani abu a gabanshi madamar wanda zai kawo masa cigaba ne na rayuwa.

Haka kuma matashin mai kimanin shekaru ashirin da bakwai yace lallai lokacin da yake neman wannan tallafi daga gidauniyar Tony Elumelu, saida ya jarabba lokuta da yawa kafin cimma nasara.

Amma Kuma yace ya zuwa yanzu babu abinda zaice sai godiya ga Allah daya basu nasara nasamun wannan abu da yanzu haka suka tabbatarma da al’umma nagarta da jajircewa wajen neman nakai.

Haka kuma shugaban kungiyar ya kuma jinjima shugaban dakin karatu na jihar Kano Dr Bichi ta yadda ya zaburar dashi tareda zama uba gareshi da jan linzaminsa lokacin neman wannan kudade.

Kazalika ya kuma hori wadanda suka samu wannan tallafi da suyi amfani da shi ta hanyar da ta dace wajen maida hankali ga abinda sukai alkawarin za suyi dasu, sannan kuma ya kara horansu da suma idan sunsamu dama su taimaki wasu al’umma dan fita daga kangin babu.

Ya kuma ce lallai kasancewar suna bukatar Kano ta zama kangaba wajen harkar kasuwanci sun shirya tsaf wajen ganin sun taimaki jama’a da suke da muradin kasuwanci a jihar Kano.

Shima a nasa jawabin yayin taron mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin samarwa matasa hanyar dogaro dakai, ya jinjinama wannan matashi daya zama zakaran gwajin dafi a fadin kasar nan.

Mai baiwa shugaban kasa shawarar Dr Muhammad Nasir ya kuma bukaci sauran masu hali da sukara sa hannun jarin su dan ragema al’umma tareda ceto mutanen mu daga kangin babu da talauci a fadin kasar nan.

Sannan yakuma nuna matukar jin dadinsa bisa namijn kokarin matashin bisa samo wannan tallafi, haka kuma ya hori wadanda suka samu wannan tallafi.

Kuma yace lallai hanyoyin da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bullo dasu dan maida matasa masu dogaro dakansu ta hanyar kananan kasuwanci da dogaro dakansu.

Sai shawarwari da suka samu daga Dr Samuel Adebayo bisa yadda yakamata jama’a sufara kasuwanci tundaga matakin farko bawai sai yatara milyoyiba a’a koda mutum yakai wannan matakin jari to bai kamata yakasance yafara maka wannan kudi dukaba lokaci guda.

Samuel yace kamata yayi nafarko ma mutum yaduba menene al’umma suke bukata tare da kawoshi akasuwa, inda yakara dacewa koda yaushe dankasuwa yakasance mai fara’a da iya tarairayar kwastoma.

Sai bayanin mai madaukakin baki Kuma shugaban cibiyar karatu na kAno state library Dr Bichi yayi matukar godiya da wannan yaro bai bashi kunyaba wajen wannan tafiya

Inda yace lallai kafin Alkamatu yazo mashi da wannan yunkuri nashi anshashi amma Kuma ya warke inda jama’a kala kala sunzo mashi da irin wannan batu amma daga inda mutum yasamu biyan bukata baka kara ganinsa

Bayan hakadai jawaba daban daban sungudana masu matukar zaburarwa da yadda matasa zasu kara kaimi kamar yadda Alkamatu ya maida hankali tareda taimakon wasu al’ummar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *