September 19, 2026

Mun yi Nasarar Haɗa Kan Al’ummar Ƙaramar Hukumar Dala -Muhmud Hassan

0

Babangida Sunusi, Kano

Kungiyar dala ina mafita qungiya ce da wasu Yan kishin karamar hukumar Dala dake jahar kano suka kirkira dan taimakama kansu ta hanya daban daban.

Dayake bayyanama Albishir manufar wannan qungiya shugaban kungiyar Mahmud Hussain Laminu yace sukan taimakawa matuka ga matasansu da masu bukatar taimako.

Kazalika yace mafi yawan ayukansu sukan dubi marayu marassa galihu da nakasassu tawajen makaranta da bukatarda suke da ita.

Mahmud yakumace lallai rashin madogara yana daya daga cikin abinda yasa akesamu matsalolin daban daban kama daga shigewa gaba dan tsira daga halaka.

Hakama yace lallai sunsamu nasarori daban daban kama daga samar da gyaran hanyar zuwa kofar ruwa zuwa gwammaja,sannan batun samarda katin dankasa ga al’umma dan samun fahimtar zama dankasa nagari.

Haka kuma yace lallai sukanyi duba da irin abubuwan da yankunansu suke bukata, haka Kuma sukan wayarma da Al’umma dala kan Wanda suka zama da kuma abinda yakamata ace sunyi masu.

Sannnan yace sunsamu damar bibiyar dukkan ayukanda wasu wakilai sukan fara daga baya sudaina amma sukan bi dan tabbatar cigabada wannan aiki.

Sannan yace yakamata gwamnati data lura kan irin ayukan wannnan kungiyata hanyar jama’a musamman yankin Kurna da mafi yawalokutan damina wasu masu gidajensu saidai su bar anguwar.

Shugaban qungiyar yakumace yazuwa yanzu dai kungiyar ta maida yara sama da dari biyu makaranta, haka Kuma yace lallai idan kadubi marakantun su yanzu haka babu makarantarda bata bukatar malamai, haka asibitoci.

Shima dayake bayani kan yadda samarda wannan kungiya Comred Abubukar Ismael D Turawa, yace lallai karatun dayayi awasu Yankuna na kudu yakarama mashi kaimi ganin yadda a kudu basu jiran gwamnati.

Haka Kuma kasancewar yadda shugaba kungiya hazikine wajen gwagwarmaya tundaga matakin farko harzuwa inda yadace.

D Turawa yakumace mafi girman nasara anan shine yadda suka haskama al’umma kan yadda yadda yadda da Wanda yakamata suzabi shugaban dazai taimaka masu alokacin dasuka zabeshi.

Yakuma bayyana godiyarsu ga dukkan wadanda suke basu hadin kai tafuska daban daban.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *