September 18, 2026

“Muna Da Rumfunan Zaɓe 602 Da Ba Masu Kaɗa Ƙuri’u A Jihar Katsina”. -Hukumar Zaɓe

0

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Ƙasa da ke Katsina Alhaji Jibril Ibrahim Zarewa, ya bayyana cewar rumfunan zabe 602 daga cikin 1750 da aka kara a Jihar sun rasa samun mutanenda zasu gudanar da zabe.

Kwamishinan na magana ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki a kan harkokin zaɓe da hukumar ta shirya kuma ya gudana a Babban Ɗakin Taro na Hedikwatar Hukumar da ke Katsina.

Makasudin taron dai shi ne, domin tattauna hanyoyinda za’a inganta yin rajistar zaɓe ta lura da cewar ana fuskantar ƙarancin aiwatar da rajistar a Jihar.

Kwamishinan Hukumar Zaben A Jihar Katsina Alhaji Jibril Ibrahim Zarewa ya bayyana cewar, Hukumar ta shirya tsaf domin gudanar cigaba da yin rijistar sabbin masu zabe a dukkan Kananan Hukumomi 34 da ke Jihar, kamar yadda Katsina Post ta rawaito.

Kamar yadda Zarewa ya tabbatar, rajistar masu zaɓen zata cigaba a Kananan Hukumomi 17 da matsalar tsaro ta shafa a Jihar.

Wakilan Kungiyoyin Fararen Hula da sauran Kungiyoyi da suka halarci taron sun bayyana cewa zasu himmatu wurin fadakar da Jama’a akan su fahimci bukatar da ke akwai na su mallaki katin zaɓen.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *