November 19, 2026

Mun Yi Allah Wadai Da Kalaman Garba Abubakar Dan Musa Akan Masarautar Maska -‘ Unity Foundation’

FB_IMG_1747847460035

Mun Yi Allah Wadai Da Kalaman Garba Abubakar Dan Musa Akan Masarautar Maska -‘ Unity Foundation

Gidauniyar haɗin kan Funtua ta nuna damuwa tare da yin Allah wadai akan wasu kalamai da wani Garba Abubakar Dan Musa ya yi dangane da batun matsayin masarautar Maska da kuma ruɗanin kirkiran sabbin masarautu a Katsina
Shugaban gidauniyar  Mannir Mohammed Suleiman ya bayya haka a wata sanarwar da ya fitar a Katsina aka rabawa manema labarai.
Shugaban wanda ya bayyana cewa wanda aka tattauna da sh a wata kafar yaɗa labarai ya bada bayanan da ba gaskiya bane game da tarihin masarautar Maska  musamman rashin kula da ƙima da tarihin masarautar da aka kafa tun ƙarni na 15
Ya ƙara da cewa, akwai buƙatar shi wanda ya yi wancan tattaunawa ya nemi tarihin masarautar Maska daga waɗanda suka san tarihi ta hanyar majiya mai tushe ba ƙoƙarin rushe tarihi ba.
Kwamarad Mannir Sulaiman ya bayyana cewa al’umma da kuma mabmobin masarautar Maska ba za su amince da irin wannan karan tsaye da ƙoƙarin ɓata suna ba.
Yana mai cewa tattaunawar tana maida hankali ne wajen bayyawa al’umma abinda ba gaskiya ba, ya ce dole ne a fadawa al’umma ainihin tarihi domin ta haka ne za a samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma
Haka kuma ya ƙara da cewa wanda aka yi wancan tattauna da shi ɗin ya nuna rashin ɗa’a da girmama masarautar Katsina.
Shugaban gidauniyar ya yi kira da kakkausar murya da a tashi tsaye wajen kare martabar tarihin masarautar saboda a barwa yan baya masu tasowa kyakkyawan tarihi.

About The Author