Mun Kawo Ziyarar Ƙarfafa Gwiwa Ne Ga Jami’an Hukumar Kwastom Na Jihar Katsina. -ACG NP Umoh
Mataimakiyar Shugaban hukumar hana fasa kwabri ta ƙasa (customs) Mista NP Umoh ta kawo ziyarar aiki a jihar Katsina domin karkafa gwiwar jami’an hukumar da kuma sabon shugaba.
Mista NP Umoh wanda ke kula da shiyar arewa maso yamma da wasu jihohi na arewa ta tsakiya, ta ce kawo ziyarar aiki a jihar Katsina na da nasaba da ƙoƙarin hukumar na ƙara kyautata dangantakar aikin a tsakanin jami’an ta.

Haka kuma ta ƙara da cewa, sun zo Katsina ne domin su karfafi gwiwar sabon shugaban hukumar AC Muhammad Sa’id domin ɗorawa daga inda tsohon shugaban ya tsaya wajen ayyukan hukumar.
Haka kuma Mista NP Umoh ta ce hukumar kwastom na yin wani shiri na fara gwajin jami’an ta akan ta’amali da kwayoyi domin ba su damar yin tunani mai kyau musamman waɗanda ke aiki akan iyakoki.

Kazalika NP Umoh ta yabawa duk shugabannin hukumar da ke karkashin kulawar shiyyar B wajen nuna ƙaimi da dagewa domin yin abinda yake daidai.
“Ina mika yabo da jinjina musamman ga hukumar kwastom din ta jihar Kano saboda irin ƙoƙarin da suka yi na cimma nasarar samun kuɗaɗen shiga tare da bin tsarin dokar aiki sannan ina jinjina wa ofishin jami’in hulda da jama’a na hukumar da ke Kano” inji ta

Sannan ta yaba da ƙoƙarin da hukumar ke yi a jihar Katsina na ganin an cimma nasara da aka sanya gaba duk da irin kalubalen tsaron da ake fuskanta musamman kan iyakoki da matsalar masu harkar fasa kwabri.
Daga karshe Misra NP Umoh ta shawarci jami’an hukumar kwastom da su kasance masu lura da kansu a ya yin aiki ta hanyar amfani da karfin basira a lokutan gudanar da aikin su na yau da kullum.

Mista NP Umoh ta samu kyakkyawar tarba daga sabon shugaban hukumar kwastom na jihar Katsina AC Muhammad Sa’id da sauran jami’an hukumar a shalkwatar hukumar kwastom da ke Katsina

