September 18, 2026

Mun Bi Sahun Uwar Jam’iyya Ta Ƙasa Wajen Gudunar da Zaɓen Shugabannin a Jihar Katsina – ADC 

FB_IMG_1775458975287

Jam’iyyar adawa ta ADC a jihar Katsina ta ce zata bi sahun da uwar jam’iyya ta ƙasa ta ɗauka ba yin zaɓen shugabannin jam’iyyar a matakin mazaɓu da ƙananan hukumomi da kuma jiha.

Matakin dai na zuwa ne a daidai wannan da ake cigaba da samun danbarwa tsakanin hukumar zaɓe ta kasa INEC da kuma jam’iyyar ADC a wani yanayi da masana ke kallon ana ƙoƙarin murkushe jam’iyyun adawa a Nijeriya.
To sai dai a jihar Katsina ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar, Alhaji Lawal Tukur Ɓatagarawa ya ce sam ba zata samo ba, wai bindiga a ruwa, kawai gwamnati na tsoron kaye ne yasa take yi masu bita da kulli.
A cewar sa, babu abinda zai dakatar da su daga gudanar da zaɓen shugabannin a matakai daban-daban saboda haka ya ce tuni sun fara shiri ba gudu kuma ba ja da baya, sai sun kai ga nasara.
Alhaji Lawal Tukur Ɓatagarawa wanda ya ce hukumar zaɓe ta kasa INEC ta yi wa hukuncin kotun daukaka ƙara gurguwar fassara dangane da karar da ke gaban kotun
“Duk wasu shirye-shiryen ƙarƙashin ƙasa da gwamnatin tarayya ke kitsawa domin ɓata mana lokaci da kawo mana koma baya a wannan tafiya Muna sane kuma zamu ɗauki mataki na hankali da shari’a” inji shi
Haka kuma shugaban ya ce suna cikin tattaunawa da lauyoyi su domin daukar matakin shari’a akan hukumar zaɓe ta kasa INEC.
Ya ƙara da cewa shirye-shirye sun yi nisa inda za a fara wannan zaɓe a ranar 09/04/2026 a kammala ranar 14 ga wata da babban taro na ƙasa (National Convention)
Shugaban ya bayyana cewa tuni suka an kare da cewa gwamnati na san yin amfani da hukumar zaɓe ta kasa INEC wajen tsorata su da kuma ɓata masu lokaci, dai dai ya ce ba za su ɗagawa kowa kafa ba, amma ba su bi tsarin doka
Daga karshe ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar haɗaka ta ADC da masoyansu da su fito a yi wannan zaɓuɓuka lafiya a kammala kamar yadda aka tsara

About The Author