September 18, 2026

Miyagun Kwayoyi: Hukumar NDLEA Ta Kama Wanda Ya Dawo Daga Kasar Brazil Da Hodar Iblis A Cikin Al’aura.

0

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA sun kama wani dan Najeriya da ya dawo daga kasar Brazil, Igwedum Uche Benson a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Ikeja Legas dauke da hodar iblis da aka boye a al’aurarsa.

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama Igwedum a filin jirgin saman Legas a ranar Litinin din da ta gabata a lokacin da ya sauka a kan jirgin Ethiopian Airlines daga Sao Paulo na Brazil ta Addis Abab, inji majiyar Popular News Hausa ta AITlive.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya hadiye kullunan hodar iblis guda 50 kafin ya tashi daga kasar Brazil sannan ya yi kashinsu a Addis Ababa inda ya mika su ga wani mutum.

Sai dai ya ce, ya kasa yin kashin sauran kullunan hodar iblis din biyu da suka rage cikin cikinshi a dakin otal da ke Addis Ababa kafin ya hau jirginsa, kuma daga baya ya yi kashinsu a ban-dakin jirgin sama a lokacin da ya tashi daga Habasha zuwa Legas.

A wani labarin kuma, Jami’an hukumar NDLEA sun kama Onyekachi Chukwuma Macdonald, wanda ake zargi da fitar da fakiti 40 na Methamphetamine da aka fi sani da Mkpuru Mmiri daga Najeriya zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya ta hanyar tashar NAHCO da ke filin jirgin saman Legas.

An kama Onyekachi ne a Estate Manacola, unguwar Alakuko da ke Legas a karshen mako, makonni uku bayan an kama Mkpuru Mmiri mai nauyin kilogiram 2.05 a filin jirgin sama kuma aka kama wakilinsa Peter Christopher Anikan a ranar 7 ga watan Yuni.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin dan asalin Ahiazu ne a karamar hukumar Mbaise ta jihar Imo ya zauna a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa na tsawon shekaru 10 kafin ya dawo Najeriya a shekarar 2019 ya fara sana’ar miyagun kwayoyi yana zaune a jihar Ogun.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *