September 18, 2026

Hukumar NECO Zata Fara Jarabawar Gwaji Ga Daliban Da Zasu Rubuta Jarabawar A Ranar 27 Watan Yunin Wannan Shekara.

0

Hukumar kula da jarabawar kammala makarantar sikandiri ta Najeriya wato NECO ta ce za a fara jarabawar gwaji ga daliban da za su rubuta jarabawar a ranar Litinin mai zuwa 27 ga watan Yunin wannan shekarar ta 2022.

Sanarwar da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Aziz Sani ya fitar, ta bukaci ma’aikatar ilimi, shugabannin makarantun sikandire da sauran masu ruwa da tsaki da su yi watsi da jita jiyar da ake yada cewa, an sauya ranar rubuta jarabawar.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, hukumar jarabawar ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don yin jarabawar cikin nasara.

Za dai a fara rubata jarabawar NECO ta shekarar 2022 a ranar Juma’a 12 ga watan Agustan wannan shekarar.

Rohotonni sun bayyana cewa, za a yima ɗaliban jarabawar akan darussa 76 a lokacin jarabawar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *