Me Yasa Jam’iyyar PDP Ke Cigaba Da Bunƙasa A jihar Katsina?
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina sun bayyana cewa daruruwan jama’a suka sauya sheka Daga wasu jam’iyyun siyasa zuwa jami’yyar PDP ta jihar Katsina.
Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke ya jagoranci bude wani babban ofishin jami’yyar a garin marabar Ƙanƙara ta ƙaramar hukumar Malumfashi.
Ofishin yakin neman zaɓen Sanata Yakubu Lado mai suna “PDP Super Elders Forum” ya damu halartar manya da ƙananan ‘yan siyasa na shiryar Funtua.
Bayan kammala buɗe ofishin da tare da karɓar waɗanda suka sauya sheƙa tagawar Sanata Yakubu Lado sun wuce zuwa ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
A ƙaramar hukumar Bakori Sanata Yakubu Lado da ‘yan tawagarsa sun ƙaddamar da gidauniya mai Maida wa Foundation wanda ta yi suna wajan taimakon jama’a.
