Miji Da Mata Sun Rasa Ransu A Katsina
Daga Zahraddeen Sirajo Abbas
Al’ummar unguwar Rahamawa da ke cikin Garin Katsina sun kwana da mummunan al’amari na mutuwar miji da mata, waɗanda suka samu ajalinsu a cikin gidan nasu da ke gurin da ake kira hayin Korama duk a cikin Unguwar ta Rahamawa
A jiya Juma’a ne 19/08/2020 da mislain 5:00 na Yamma Mutanen Unguwar Rahamawa suka kwana da mutuwar Miji da Mata, Mijin mai suna Murtalad Muhammad (Over) da Matarsa Shamsiyya, makusantansu sun sheda mana cewa “auran nasu yanzu yana da Shekara daya da wata shidda suna zaune lami lafiya shi da Matarsa”.
Da wakilinmu yake zantawa da kanin da Mijin ya sheda mana cewa “Marigayi murtana yaje Masallacin Juma’ah jiya, da yake ana kwarara Ruwan Sama a haka aka yi Sallah duk fadin Jahar ta katsina, Shi ya ke Limamin Masallacin Auwalu Buba Masallaci ya kuma mai do shi, daga nan ya wuce Gidansa.
Chen wajen misalin 4:00 na Yamma wani abokinsa ya kirani cewa in bashi lambar Murtala ya kira wayarshi bai dauka ba, na tura masa ya kira ba’a dauka ba, dayake bamu da nisa da Gidansa, sai ga Kanin Matarsa sun biyo ta gidanmu suka ce sun je gidan sun yi ta buga kofa shiru, na kira wayarshi ba’a dauka ba.
Mamarmu tace kaje ka gani ko lafiya, nan take muka je gidan muka buga shiru, na tuntuda Kanena ya shiga ya bude, ashe suna cikin wani Daki yana kulle muka buda tagar dakin muka hango kafarsa, cikin sauri muka bude dakin muka samesu alamu basu da rai, muka yi gaugawar jai su General Hospital, ana dubawa aka sheda mana cewa sun ransu.
Haka zakalika an yi Jana’izar bayjn Allahn da mislin 10:00 na safiyar yau Asabar kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada, Jama’a daga wurare daban daban suka halarci Jana’izar, tare da yi masu Addu’ar samun rahamar Allah (S)”
“An shaidi Marigayin da ƙoƙarin neman na kansa sannan yana zaune da Mutane lami lafiya, wasu kuma na cewa yana da sakin fuska da walwala, a gefe guda kuma mafi yawan mutanen suna cikin jimami da halin tausayi, wasu kuma na ta kukan rabuwa.
