September 18, 2026

Mata 5000 Suka Amfana Da Tallafin Miliyan 20 Da Atamfofi Daga G15 A Zamfara

IMG-20250510-WA0013

Daga Hussaini Yero

Kungiyar G15, da ke goyan bayan, ayyukan cigaba da gwamna Dauda Lawal a fadin Jihar Zamfara,ta rabawa mata dubu biyar, miliyan ashirin da Atamfofi a cikin Karamar Hukumar Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

A Taron manaima labarai da Kungiyar G15 tayi , Karkashin Jagorancin Shugaban Kungiyar,Hon Mannir Haidara , Shugaban Karamar Hukumar Kauran Namoda , ya bayyana cewa, Kungiyar G15, kowace Karamar Hukumar tana da wakilcin muyi daya sai kuma Gusau tana da mutum biya dan haka ya zamo mutum sha biyar kenan muka kirata da G15.

Kuma G15 ta karade Karamar Hukumomi sha hudu da muke da su, dan tallafawa mata da Sutura da kudin jalin Sana’a.wanda a yau muka kammala da Karamar Hukumar Gusau, Inda muka ba Mata dubu biyar miliyan ashirin da Atamfofi,mai dara gwamna Dauda ya Jagoranci Kaddamarwa .inji Hon Haidara.

” Hon Haidara ya kuma tabbatar da cewa yanzu haka G15 ta yunkuro wajan bada tallafi ga Matasa da Matasa masu kanan sana’a dan dogara da kansu.

Akan haka muke kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su ci gaba biyayya ga gwamnatin Zamfara Karkashin Jagorancin gwamna Dauda dan samun Nasara kammala ayyukan da ya dauko na alhairi ga al’umma.da Kuma yiwa Gwamnatin addu’ar dan samu dawamamen zaman lafiya a Jiha mu ta Zamfara da Kasa baki daya.

About The Author