November 17, 2026

Gidauniyar Mangal Ta Dauki Nauyin Yi Wa Mutum 12,300 Masu Cutar Ƙaba Aiki A Katsina 

IMG-20250510-WA0006

Fiye da mutum dubu sha biyu (12,300)ne masu ɗauke da cutar ƙaba gidauniyar Alhaji Ɗahiru Mangal ta yi wa aiki kyauta a Katsina

Kamar yadda ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na gidauniyar Malam Hussaini Kabir ya shaidawa manema labarai a Katsina a lokacin ƙaddamar da aikin tiyatar kashi na biyu.
Ya bayyana cewa gidauniyar tana gudanar da wannan aiki ne kyauta ga marasa karfi duk bayan wata uku tun daga lokacin da aka kafa gidauniyar a shekarar 2013
Ya ƙara da cewa mutane 500 zuwa 600 ne suke amfana da wannan aiki na cutar Ƙaba duk bayan watanni uku da ake gudanar da aikin.
“Waɗannan Ayyuka da muke yi ba wai sun tsaya bane akan mutanen Katsina ba, harda makwabtan jihohi suna amfana da wannan gudunmawa” inji Malam Hussaini.
A cewar sa, baban dalilin da yasa suke wannan aiki shi ne, domin a ragewa al’umma musamman masu ƙaramin karfi wahalwalun da suke sha wajen neman lafiya.
Malam Hussaini Kabir ya yi kira ga sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su bada ta su gudunmawa wajen irin wannan aiki ta yadda za su taimakawa ƙoƙarin gwamanti akan harkokin kiwon lafiya.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da wannan taimako na aikin ƙaba sun yaba da ƙoƙarin wannan gidauniya inda suka ce hakan zai taimakawa ƙoƙarin gwamanti da sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su yi ko yi da wannan gidauniya.
Kamar yadda suka bayyana da kan su, cewa wannan aiki yana matuƙar taimaka masu wajen rage wahalhalu da suke fama da mu a wannan yanayi na matsin tattalin arziki.
Kazalika wannan gidauniya tana yin aikin ido kyauta ga masara karfi a fadin jihar Katsina.

About The Author