September 17, 2026

Masarautar Katsina Ta Warware Sarautar Makaman Katsina

0

Majalisar Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ta dakatar da makaman Katsina, Hakimin Bakori Alhaji Sule Idris Nadabo daga sarautar shi biyo bayan bincike da gwamnatin jihar Katsina ta gudanar akan shi.

A wata takardar da aka fitar ga manema labarai an bayyana cewa gwamnatin jihar ce ta Offishin Gwamnan Jihar ta tabbatar da ƙorafe ƙorafen ko zarge zargen da akeyi akan basaraken da suka shafi yanayin rashin tsaro a yankin Masarautar shi, bisa wannan dalilin aka tuɓe mashi rawanin shi na Hakimcin Bakori.

Takardar wadda Ƙauran katsina hakimin Rimi Alh. Aminu Nuhu Abdulkadir ya sanyawa hannu ta bayyana cewa, Majalisar Masarautar Katsina ta yanke Shawarar Sallamar Makaman daga Muƙamin shi daga ranar Alhamis 19/01/2023.

Idan dai ba’a manta ba cikin watan Nuwamban Shekarar da ta gabata ne aka dakatar da hakiminna Bakori bisa zarge zargen da suka shafi matsalar rashin tsaro.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *