November 18, 2026

Gangamin Yakin Neman Zaɓen APC A Ƙaramar Hukumar Gumi Ya Samu Tagomashi

0

Daga Hussaini Ibrahim

Dubban magoya bayan jam’iyyar APC ne a ƙaramar hukumar Gumi da ke jihar Zamfara suka karɓi jirgin yakin neman zaɓen gwamna Bello Matawalle a karo na biyu a jiya Alhamis.

Taron yakin neman zaɓen ya kuma samu halartar ɗaukacin tsohon gwamna, Mahmud Aliyu Shinkafi, da tsaffin mataimakan gwamnoni, Ministoci, Kakakin Majalisa da mataimakansu da kuma dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Da yake jawabi a wajen taron, gwamna Bello Matawalle ya yaba wa dimbin magoya bayan da kuma dimbin jama’ar jam’iyyar APC da suka halarci taron da ya bayyana a matsayin wanda ke nuni da nasarar APC.

Ya yabawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC Gumi bisa yadda suka yi gangamin neman jam’iyyar APC na ta samu nasara a zaɓe mai zuwa.

“Gwamna Matawalle ya ɗauki alwashin samar da wasu ayyuka a ƙarƙashin gwamnatin APC na cigaban ƙaramar hukumar Gumi idan aka sake zaɓar sa a karo na biyu.

Matawalle ya ƙara da cewa “Ina kira gare ku da ku zaɓi dukkan ‘yan takarar APC a kowane mataki.” .

Gwamnan ya kuma yi alƙawarin yin bakin ƙoƙarinsa wajen inganta harkokin tsaro, ilimi, fannin lafiya da kuma tattalin arzikin jihar baki ɗaya.

Tun da farko shugaban kwamitin yakin neman zaɓen Matawalle karo na biyu, tsohon gwamna Abdul’aziz Yari ya yabawa al’ummar ƙaramar hukumar Gumi bisa kauna da goyon bayan da suke baiwa jam’iyyar APC.

Yari ya ce, APC ta ci gaba da zama jam’iyyar siyasa mai karfi a jihar domin ‘yan adawa ba su taɓa cin zaɓe a jihar ba.

Ya bukaci masu zaɓe da su kada kuri’a ga Tinubu, Matawalle, ‘yan majalisar tarayya da na jihohi a zaɓen da za a yi a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 11 ga Maris, 2023.

Yari ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da su ci gaba da ba da hadin kai tare da tabbatar da yin aiki don samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *