September 18, 2026

Majalisar Wakilai ta ki amincewa da kudirin yin wa’adi ɗaya na shekara 6 ga shugaban ƙasa da gwamnoni

0
FB_IMG_1732199611004

Majalisar Wakilai ta ki amincewa da kudirin yin wa’adi ɗaya na shekara 6 ga shugaban ƙasa da gwamnoni

Majalisar Wakilai ta kasa ta ki amincewa da karatu na biyu na kudirin da ke neman samar da wa’adin shugabancin shekaru shida kacal ga shugaban kasa da gwamnoni.

Majalisar ta yi watsi da kudirin ne yayin zamanta na ranar Alhamis.

Kudirin dai an gabatar da shi ne karkashin jagorancin dan majalisar, Ikenga Imo Ugochinyere tare da sauran mambobi 33.

An gabatar da kudirin domin karatu na biyu ne daga babbar mai daukar nauyin sa, Ugochinyere, sannan aka goyi bayan hakan.

Sai dai, yayin da Kakakin Majalisar, Abbas Tajuddeen, ya mika kudirin don kada kuri’a ta baki, muryoyi masu cewa “A’a” sun fi yawa daga mambobin majalisar.

A karshe, Kakakin ya sanar da cewa wadanda suka ce “A’a” sun yi rinjaye, wanda hakan ya nuna cewa kudirin bai samu amincewa ba kuma ya fadi a karatu na biyu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *