Mai Kwarmata Bayanan Sirri: Yadda Emefiele Ya Sa Aka Tsare Ni Sama Da Kwanaki 100 Saboda Na Bayyana Zambar Masayar Kuɗaɗen Waje.
Dokta George Uboh, shugaban kungiyar George Uboh Whistleblowers Network (GUWN), ya bayyana yadda aka kama shi tare da tsare shi na tsawon kwanaki 101 a shekarar 2019 bayan da ya fallasa badakalar damfarar masayar kuɗaden waje karkashin gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele, wanda ake jerangiya akan shi yanzu.
Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta Dailytrust ta bayyana.
Uboh ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan dakatar da Emefiele da kuma bada umarnin gudanar da bincike.
“Kungiyar George Uboh Whistleblowers Network ta fallasa almundahana da Emefiele ya yi game da zamba na sama da dalar Amurka biliyan 3 ta wasikun da aka rubuta wa Emefiele a ranar 1 ga Afrilu, 2019.
“A ranar 15 ga Mayu, 2019, ranar da Emefiele ya gurfana gaban majalisar dattawa domin tantancewa kan wa’adinsa na biyu, an kama ni a ofishina na Maitama. An tsare ni tsawon kwanaki 101 bisa bata sunan Emefiele.
Babban alkalin kotun Abuja na wancan lokacin, Ishaq Bello ya ki sauraren bukatar belina. DIG Mike Ogbizi ya ƙi bada ni beli bayan na cika sharuddan belin da jami’an tsaro suka a babban sashen bincike na CID.
