Kwamandan C-Watch Ya Zargi Sojoji Da Haɗa Baƙi Da ‘Yan Bindiga a Katsina
Kwamandan C-Watch Ya Zargi Sojoji Da Haɗa Baƙi Da ‘Yan Bindiga a Katsina
Daga Hussaini Ibrahim
Kwamandan da ke kula da al’ummar jihar Katsina a karamar hukumar Dandume Manjo AL Ibrahim Rtd, ya zargi sojojin da aka tura yankin da hada baki da ‘yan bindiga da suka addabi yankin.
Manjo Ibrahim Rtd ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a garin Funtua hedikwatar karamar hukumar Funtua a ranar Litinin
A cewarsa, sojojin na yin zagon kasa ga kokarin aikin hadin gwiwa da suke yi, inda ya ce a baya-bayan nan ne rundunar KCWC ta jihar Katsina Reshen Dandume karkashin kulawar sa ta kama daya daga cikin masu samar da makamai da alburusai na kauyen Dankolo da ke karamar hukumar Dandume tare da mika mai laifin ga sojojin da aka tura yankin Machika amma sai suka fahimci cewa sojojin sun sake shi ba tare da wani sharadi ba.
Ya kuma bayyana cewa dakarun da ke yankin suna yi masa barazana.
“Rayuwata na cikin barazana daga sojoji a karamar hukumar Faskarida Dandume kuma ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakin gaggawa a kansu”. Yace
“Ina so in jaddada cewa duk abin da ya faru da ni, iyalina da jami’ai na, sojojin za su fuskanci hukunci saboda suna matukar barazana ga rayuwar mu”.
“Ya kara da cewa, ina zargi wani Kyaftin Rabiu da Laftanar Friday Jeremiah da yin zagon kasa a yakin da ake yi da ‘yan bindiga a kananan hukumomin Sabua da Dandume a jihar, inda ya yi kira ga babban hafsan soji, maiba Shugaban Kasa Shawara akan tsaro na da kuma ministan tsaro da su kafa kwamitin da zai binciki su.
“Ina kira ga babban hafsan sojin Kasa, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da ministan tsaro da su duba ayyukan sojojin da aka tura kananan hukumomin Sabua da Dandume domin suna daya daga cikin manyan kalubalen da muke fuskanta a yakin da ake yi da ‘yan bindiga a yankunan”.
‘A cewarsa, sojojin ba su shirya yin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro a yakin da ake yi da ‘yan bindiga a yankunan ba.
“A shirye muke mu yi aiki kafada da kafada da dukkan jami’an tsaro da abin ya shafa a yankunanmu domin dakile ‘yan ta’adda amma babban abin da ke damun mu shi ne, sojojin da aka tura yankunan ba sa taimakawa al’amura saboda muna zarginsu ne ta hanyar hada baki da wadannan ‘yan ta’addan da ake tsoro”.
