Kwalejin Samkwang Tabi Sahu Wajan Samar da Ƙwararu Ma’aikatan Lafiya A Zamfara
Daga Hussaini Ibrahim
Shugaban Kwalejin Kiwon Lafiya da kimiya ta Samkwang Samaila Hussaini ya bayyana cewa, sun samar da Kwalejin ne dan amfanar al’ummar Jihar Zamfara wajan samar da ma’aikatan lafiya kwararu.
Samaila Hussaini ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Ofishin sa da ke Takama cikin Gusau , Baban Birnin jiha Zamfara.
Shukuran Samkwang ya bayyana cewa,ganin yadda alumma ke da bukatar Malaman lafiya a wannan jiha ta mu kuma dalibai da dama wadanda suka kamma Sakandire suna shira’awar karatun lafiya ,wasu Talakawa ne basu iya kai ‘ya’yan su nesa ba, sabo da tsadar rayuwa kuma gashi yaran na su suna da hazaka sosai ya bamu kwarin gyuwar samar da kwalejin kimiyya lafiya da fasaha mai suna Samkwang.inji Shugaban nata.”
“Kuma wannan kwalejin tayi hadin gyuwa da Kwalejin Kimiya ta Lala dan samun ingantace shedar kammala karatun lafiya.
Kuma muna kwasakwasai wadanda suka hada da Health Information da Medical Lab da sauran su.inji Shugaban Kwalejin.
Da ya koma kan Iyayan Shugaban Kwalejin ya yi kira ga Iyayan yara masu shia’ar karatun lafiya da su kai yaran su makarantu masu inganci dan kada su fada makarantun bogi.
Da ya koma kan dalibai kuwa Shugaban yayi kira ga dalibai da suji tsoran Allah su maida hankali wajan koyan abubda su kazoyi mu samman karatun lafiya karatun wannda ya ke da hadari dan rayuwar alumma a hannunsa ta ke.dan haka su meda hankali su koyi abunda aka karantar da shi dan ceto alumma masara lafiya da ya ke dubawa.
