September 17, 2026

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Gaba Da Dan Achaba A Abuja.

0

A yammacin ranar Talata ne ambaliyar ruwa tayi awon gaba da wani dan achaba wanda ba a san ko wanene ba a yankin Chikakore da ke Kubwa, a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru ne bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.

Dan achabar wanda ya yi watsi da kiraye-kirayen da ‘yan kallo suka yi masa, ya yi yunkurin tsallaka kwalbatin da ta hada wani bangare na al’umma.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *