September 18, 2026

Kurya Ya Zama Dan Takarar Majalisar Jihar AJam’iyyar PDP Na Kauran Namoda A Zamfara

IMG-20250723-WA0016

 

 

Daga Hussaini Yero

Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta bayyana Muhammed Lawal Kurya Wanda yayi nasara a zaben cike gurbi da aka kammala a Kaura Namoda ta Kudu.

Hakan ya biyo bayan janyewar wasu da dama daga cikin masu neman tsayawa takara, domin samun dan takara daya tilo.

Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, Naziru Ibrahim Rufa’i ne ya bayyana hakan a hira da manema labarai a Hedikwatar Jamiyyar da ke Gusau.

Sakataren ya kara cewa, ‘yan takara 14 ne suka mika wa ofishin jam’iyyar PDP da ke jihar takardar bukatarsu tun da farko, a hankali, 4 ne kawai suka sayi fam din tsayawa takara a jam’iyyar domin yin zaben fidda gwani ,inji Sakataren “.

“Sakataren jam’iyyar ya bayyana cewa bayan fitar da jadawalin zaben fitar da gwani daga hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta, sakatariyar jam’iyyar ta Kasa daga Abuja ta umurci jam’iyyar PDP ta jihar Zamfara da ta fara shirye-shiryen tunkarar zaben ‘yan majalisar dokokin jihar Kaura Namoda ta Kudu.

A cewarsa, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a yankin, sun zauna da ‘yan takara 4, inda suka cimma matsaya kan barin Muhammed Lawal Kurya ya tsaya takarar a matsayin dan takarar PDP.

Sai dai ya bayyana cewa, zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP na zaben Kaura Namoda ta Kudu ya samu kulawar kwamitin mutane 5 da suka fito daga Sakatariyar jam’iyyar ta Kasa karkashin jagorancin Nasir Mohammed da wakilin INEC a jihar da kuma wani kwamiti daga ofishin PDP na jihar.

Sakataren ya ba da tabbacin samun nasarar lashe zaben da ke tafe, domin a cewarsa, a bayyane yake ga kowa a jihar Zamfara cewa nasarorin da gwamna Lawal ya samu musamman biyan fansho da kuma kyauta ga duk ma’aikatan jihar da suka yi ritaya wanda ya kai sama da Naira biliyan 13, zai zama daya daga cikin dalilan da masu zabe a yankin za su kada kuri’ar zaben dan takararmu.

About The Author