Kungiyar Tsaro Ta ‘National Task Force’ Ba Hukuma Ko Ma’aikatar Gwamnati Ba Ce, Cewar Sanata Ahmad Babba Kaita
Sanatan mai wakiltar yankin arewacin Katsina a zauren majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Babba Kaita, ya ja hankalin al’umma akan inganci da sahihanci hukumar tsaro ta ‘The National Task Force’.
Sanata ya yi wannan jan hankalin a yau Litinin a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa babu wata hukuma ko ma’aikata a gwamnatin tarayya mai irin wannan sunan da doka ta amince da ita.
“Ya zamto dole in yi ɗan tsokaci ga ɗimbin mutanen da su ke ta kiraye – kiraye kan wata Organization Task Force”.
“Babu wani Organization mai suna haka da doka tai amince da shi (Recognizing) a cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan a yau ɗin nan. Dan haka (Therefore), mu daina yaudarar kanmu kan takardun ɗaukar aiki (Employment Letters) da ake ta saidawa al’umma hakazalika ma waɗanda ake badawa kyauta“.
A ɗan tsakanin nan dai ƴan siyasa na rabawa magoya bayansu takardun kama aiki a wannan ƙungiyar tsaro.
Ƙungiyar tsaro dai ta National Task Force, ƙungiya ce da ke neman zama ɗaya daga cikin hukumomin tsaro a Najeriya. Haka kuma aikin da kungiyar ke son ta aiwatar su ne daƙile safarar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma fasa bututun man fetur a yankin Neja Delta.
