September 16, 2026

Babu yadda za’ai ace yan ta’adda sunfi karfin jami’an tsaro — Kwankwaso

0

Babu yadda za’ai ace yan ta’adda sunfi karfin jami’an tsaro — Kwankwaso
Tsohon ministan tsaron Nigeria, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana takaicinsa akan yadda lamuran tsaro ya tabarbare musamman a yankin Arewacin Nigeria, inda yace lokaci yayi da za’a ajiye batun PDP ko APC ko wata jam’iyya a gefe, a hada kai waje guda domin ayi yaki da matsalar, tunda dai yanzu abin ya damu kowa.
Cikin wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC, Kwankwaso yayi kira ga gwamnatin tarayya akan tayi kokari wajen samar da ingantattun kayan aiki ga jami’an tsaro don yaki da yan ta’adda, da kuma basu duk wani kwarin gwiwa don aikinsu, kasancewar yan ta’addan basu da yawan da jami’an tsaro ke dashi, domin a cewar Kwankwaso ko a baya bayan nan kusan yan sanda sama da dubu talatin aka tura Anambra don kula da zaben gwamna, inda yace kamata yayi a wuce dasu Zamfara, Sokoto, Kebbi ko sauran inda ake da irin wancan matsaloli.
Har ila yau, Kwankwaso yace Allah ya bashi wata dama a baya, ya zauna da sojijin Nigeria na kasa, na sama dana ruwa, yasan kwazonsu da kuma horon da suka samu, yana mai tabbatar da cewa zasu ci nasara akan yan ta’adda idan sun samu goyon baya, tunda dai ta’addan an san su, wasu ma sunyi suna fiye da wasu manyan jami’an tsaro a Nigeria, kuma ko shugaban kasa ya fada ko bai fada ba, aikin jami’an tsaro ne wannan, kowa ya sani, a cewarsa.

Nasara Radio 98.5 FM

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *