September 18, 2026

Kungiyar SAI DA LAFIYA ta taimakon Masu Taɓin Hankali da Marayu ce. – Gunduwawa

IMG-20260208-WA0021

DAGA MUKHTAR YAKUBU 

 

A ƙoƙarin tallafawa masu taɓin hankali da da marayun da suke gararamba a kan tituna kungiyar SAI DA LAFIYA a ƙarƙashin shugabancin injiniya Ibrahim Sale Gunduwawa ta yi wani zagaye a cikin birnin Kano.

 

Zagayen dai ya kewaya wasu da cikin unguwanni Kano a ranar asabar ɗin nan domin bayar da gudummawa ga masu larurar tabin hankali da kuma marayu domin ceto rayuwar su daga halin da suka samu kan su a ciki.

 

Inda ‘yan kungiyar suke bi kan tituna suna kama masu taɓin hankali suna yi musu aski da wanka su kuma ba su sabon kaya su saka tare da ba su abincin da za su ci.

 

Anan su ma marayu ba a bar su a baya ba domin kuwa an yi masu makamacin haka daidai da bukatar su.

 

Wakilan mu ya nemi jin ta bakin shugaban ƙungiyar ta SAI DA LAFIYA injiniya Ibrahim Sale Gunduwawa a game da yadda suke gudanar da aikin na su, inda ya bayyana cewar “Ita wannan kungiya ta mu aikin ta shi ne idan muka fito duk inda muka samu mara lafiya za mu yi masa aski da wanka mu canza masa kaya, sannan sai mu saka a Soshiyal Midiya idan Allah ya sa ‘yan uwan sa sun gani suka yi mana magana, to mun san wajen da muka same shi.

 

Sannan idan kuma an samu wanda zai ɗauki nauyin magani ko na mutum ɗaya ko biyu za mu kai su asibiti ya biya kudin magani. A cewar sa

 

Da muka tambaye shi ko tsawon wane lokaci suka shafe suna gudanar da aikin tare da irin nasarorin da suka samu ya ce ” A yanzu mun kai kusan shekara kuma mun samu nasarori yi wa mutane da yawa, muna nan ɗauke da hotunan su da bayanan su, wasu ma sun samu lafiya.

 

Kuma Alhamdulillah muna samun ci gaba, musamman idan ka ga addu’a da mutane suke yi mana, kuma a yadda muke ganin mutane idan mun fito suna murna da hakan hakan yana ƙara mana karfin gwiwa, kuma akwai wani da muka samu ya dauki nauyin mutane shida aka yi musu magani.”

 

Daga karshe ya yi kira ga gwamnati da sauran jama’a da su shigo a yi wannan aikin da su, saboda zuwa yanzu duk abubuwan da suke yi da kuɗin su suke yi don haka ya nemi gudummawar gwamnati da jama’a wajen bada tasu gudummawa don a yanzu ko abin hawa ba su da shi sai dai babura masu kafa uku da suke ɗauka idan za su tafi aikin a kowanne sati, don haka muna fatan Jama’a za su shigo a yi da su domin gudanar da aikin cikin saukin da za a samu nasarar da ake bukata.”

About The Author