Ku Zo Mu Yi Aiki Tare: Kiran Kwamishina Alhaji Isah Muhammad Ga Shuwagabannin Ƙananan hukumomin Jihar Katsina
An yi Kira Ga Ƙananan Hukumomi Da Su Goyi Bayan Ma’aikatar Ayyuka Na Musamman Domin Cimma Nasarar Gwamnatin Dikko Raɗɗa
Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka na musamman ta jihar Katsina Alh Isah Mohammed Musa ya yi wannan kira ga ƙananan hukumomi da su ba ma’aikatar haɗin kai domin cimma buri da manufofin gwamnatin jiha ƙarƙashin jagotancin Gwamna Mal. Dikko Umaru Raddah.
Kwamishinan yayi wannan kira ne a Karamar Hukumar Daura a yayin ƙaddamar da aikin rabon kayan abinci da gwamnatin Jaha ta samar ta hannun ƙananan hukumomi don rage radadin halin da al’umma ke a ciki.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai aka ƙaddamar da Shirin bayar da tallafin kuma kwamishinan ya gamsu da tsare tsare-tsaren da Karamar Hukumar tazo da su don ganin cewar an yi rabon yadda ya kamata.
Tun da farko dai, Isa Mohammed Musa ya nuna jin dadinsa dangane da nagartar kayan hatsin da aka sawo tare da yin kira ga wakilan akwati da su yi gaskiya domin sauke amanar da aka dora ma su.
Bayan haka, ya soki lamirin wasu da ke kiran gwamnati da ta sayar da hatsin a maimakon bayar da tallafi.
An dai gudanar da rabon ne a farfajiyar sakatariyar Karamar Hukumar.
