Ku Bamu Dama Domin Kakkaɓe ‘Yan Ta’adda, Cewar Sojoji.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ba za ta sake yin afuwa ba ga ‘yan bindiga da ke addabar shiyyar Arewa maso Yamma na kasar nan, inda ta nemi gwamnonin su bada dama don kawar da ‘yan ta’adda.
Rundunar ta gargadi masu aikata laifukan da su bar kasar nan, inda ta ce za a sa masu ido da kuma hana su shiga sauran sassan kasar nan idan suna yunkurin tserewa daga yankin Arewa maso Yamma, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.
Shugaban hafsan sojin kasa, Maj.-Gen. Taoreed Lagbaja, wanda ya bayyana hakan a hedkwatar rundunar da ke Abuja, yayin da ya ke karbar bakuncin gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira ga gwamnonin da su baiwa sojoji dama don kawar da duk wasu masu aikata laifuka.
“Gwamnan ya ce, ina ganin akwai bukatar mu duba shirin afuwa. Masu aikata laifukan basu tuba. Don haka batun afuwa ya samar da damar sake haɗa kansu da yin hare hare,” inji Lagbaja.
Bayanin hafsan hafsan sojin ya biyo bayan kiraye-kirayen da tsohon gwamnan jihar, Sani Yerima ya yi a kwanakin baya na cewa a yi wa ‘yan bindiga afuwa.
Ya roki shugaban kasa, Bola Tinubu ya tattauna da ’yan ta’adda da ke a jihar Zamfara da sauran sassan yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.
Yerima ya ce tattaunawar da ya ke bada shawara, ta yi daidai da abin da gwamnatin tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ta yi da tsagerun Neja Delta, wanda ya haifar da shirin yin afuwa.
