September 18, 2026

Kotun Kolin Najeriya Ta Hana Gwamnati Daina Amsar Tsoffin Kudi.

0

Kotun kolin Najeriya ta hana gwamnatin tarayya tilasta wa’adin da aka dibar ma tsoffin kudin Naira.

Babban Bankin Najeriya wanda ya sake fasalin kudin Nairar, da farko ya sanya ranar 31 ga watan Janairu a matsayin wa’adin daina amsar tsoffin takardun kudin.

Sai dai an tsawaita wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu bayan matsin lamba akan gwamnatin tarayya da bankin.

A makon da ya gabata ne gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya ce bankin ba ya tunanin tsawaita wa’adin.

Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batun, inda shugaban ya bukaci su ba shi kwanaki bakwai domin ya duba lamarin.

Amma gwamnatocin jihohin Kaduna, Kogi, da Zamfara sun garzaya kotu domin kalubalantar babban bankin.

A hukuncin da ya yanke ranar Laraba, kwamitin mutane bakwai karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro ya dakatar da matakin na gwamnatin tarayya.

Kotun kolin ta umarci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su ci gaba da yin mu’amala da tsofaffin takardun kudin har zuwa lokacin da za a yanke hukunci a kotun kolin ranar 15 ga watan Fabrairu, a cewar majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *