September 18, 2026

Kotu Ta Wanke Tare Da Sallamar Jang Daga Zargin Almundahanar ₦6.3bn.

0

Wata babbar kotun jihar Filato, a ranar Litinin da ta gabata a Jos, ta wanke tare da sallamar Sanata Jonah Jang da Yususf Pam daga zargin cin hanci da rashawa na Naira biliyan ₦6.3 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa ta EFCC) ta shirya a kansu, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.

Jang, tsohon gwamnan Filato da Yusuf Pam, wanda tsohon kashiya ne a ofishin sakataren gwamnatin jihar, an fara yi masu shara’a tun ranar 4 ga watan Mayun 2018.

Hukumar EFCC ta gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu kan tuhume-tuhume 17 da suka shafi karkatar da kudaden jihar.

Alkalin kotun, Mai shari’a Christen Dabup, wanda ya yanke hukuncin, ya ce kotun ba ta samu Jang da Pam da wani laifi ba.

“Kotu ba ta sami wadanda ake tuhumar da laifi ko daya ba daga cikin tuhume-tuhumen da ake masu, saboda haka aka wanke su tare da sallamar su,” in ji ta.

Da lauyan da ke kare wadanda ake tuhuma Mike Ozekhome ke mayar da martani kan hukuncin, ya ce kotun ba ta same su da laifin komai ba a cikin tuhume-tuhume 17 da ake masu.

Ozekhome ya ce zargin EFCC ba komai bane illa karya, ba hujjar cewa tsohon gwamnan soji na Benue ya karkatar da wadannan kudaden zuwa wani aiki na kashin kai ba.

“Don haka a zahiri tsakanin ranar 4 ga watan Mayun 2018 zuwa 2 ga watan Satumba, wannan mutumin da ya yi wa jihar hidima da gaskiya yana fuskantar azaba mai tsanani da wahala tsawon kusan shekaru hudu da rabi na jarabawa da kunci.

“Amma a yau adalci ya fito, kotu ta gano cewa tsohon gwamnan bai saci ko Kobo a asusun gwamnatin Filato ba.

“To ina wannan kud’in da kuka ce wannan mutumin ya sace?” Ya tambaya.

Ozokhome ya ce babu wata dake nuna cewa tsohon gwamnan jihar Plateau ya wawure kudin da aka ce na bashi ne aka ciyo daga babban bankin Najeriya.

A cewarsa, akwai shaidun da ke nuna cewa an yi amfani da kudaden yadda ya kamata tare da tabbatar da duk shugabannin gwamnati da Majalisar Dokokin Jihar Filato sun amince da su a karkashin wata doka da ta ba da dama.

Lauyan hukumar EFCC, Oluwaleke Atolagbe ya ce ba su sami rubutaccen kwafin hukuncin ba.

Atolagbe ya ce za su sake duba hukuncin su ga ko akwai dalilan daukaka kara.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *